✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin da aka kai min ya saba yarjejeniyar zaman lafiya —Atiku

Ya yi tir da harin ne a yayin ziyarar ban girma da ya kai wa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida a…

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce harin da aka kai wa jerin gwanon motocin yakin neman zabensa a Maiduguri keta yarjejeniyar zaman lafiyar da kwamitin wanzar da zaman lafiya na kasa ya sa ’yan takara suka sanya hannu a kai ne.

Atiku ya yi zargin harin ba zai rasa alaka da wasu shugabanin siyasa ba da suka dauki nauyin bata-garin da suka aiwatar da shi.

Ya yi tir da harin ne a Mina, Jihar Neja, a yayin ziyarar ban girma da ya kai wa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida a ranar Juma’a.

Atiku na tare da rakiyar Gwamnan Jihar Delta kuma abokin takararsa, Ifeanyi Okowa da Gwamna Darius Ishaku na Taraba da Aminu Waziri Tambuwal na Sakkwato da Sule Lamido na jihar Jigswa da sauran su.