Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya soke bikin Ranar Dimokuradiyya ta bana domin girmama wadanda suka rasa rayukansu a lokacin wani hari da aka kai a Cocin St. Francis Catholic a garin Owo a Lahadin da ta gabata.
Gwamna Akeredolu ya bayyana haka ne a wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar.
- ASUU ta yi watsi da tayin tallafi don ta janye yajin aiki
- Batun zaben abokan takarar Atiku da Tinubu ya tayar da kura
A cewarsa, an soke bikin ne domin bayar da dama ga jama’ar Jihar Ondo su yi zaman mokokin wadanda aka kashe.
Akalla mutum 40 ne aka tabbatar da sun rasu a yayin harin da aka kai, inda sama da mutum 120 kuma suka samu raunuka.
ISWAP ce ta kai hari Coci a Ondo —Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce ’yan ta’addan kungiyar ISWAP ne suka kai hari kan Cocin Katolika da ke garin Owo na Jihar Ondo.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, lokacin da yake yi wa manema labaran Fadar Shugaban Kasa jawabi, jim kadan bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Kasa.