✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin bom ya kashe mutum 21 a masallaci a Afghanistan

An garzaya da mutum 27 asibiti, ciki har da kananan yara biyar bayan harin masallacin

Akalla mutum 21 sun rasu, wasu 33 kuma suka jikkata a wani harin bom a wani masallaci a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.

Hukumomin Afghanistan sun ce an kai harin ne a yammacin ranar Laraba, kuma abin da ya fashe din ya lalata gine-gine da ke kusa da masallacin.

Asibitin Emergency wanda wata kungiyar jinkai daga kasar Italiya ke gudanarwa a Kabul ya ce mutum 27 ne aka kai masa, ciki har da kananan yara biyar, bayan sun samu rauni a harin masallacin.

Daraktan Asibitin a Afghanistan, Stefano Sozza, an kawo mutum biyu asibitin a mace, wani daya kuma ya rasu a dakin kulawa ta gaggawa.

Kakakin ’yan sanda, Khalid Zadran ya ce babu wanda ya yi ikirarin kai harin, amma hukumomin kasar na gudanar da bincike kan lamarin.

Gwamnatin Taliban a Afghanistan dai ta ce tana kokarin tabbatar da tsaro a kasar tun bayan da ta karbi mulkin kasar a shekarar da ta gabata.

Bayan komawar Afghanistan hannun Taliban an samu raguwar ayyukan ta’addanci da hare-hare da tashe-tashen hankula.

Duk da haka, a baya-bayan nan an kai wasu manyan hare-hare a biranen kasar, ciki kuwa har da wanda kungiyar IS ta yi ikirarin kaiwa.

Kawo yanzu akalla mutum 140 ne suka rasu a hare-haren bom da aka kai wa mutane a masallaci tun bayan dawowar kungiyar hannun kungiyar.

A ranar Litinin 15 ga watan Agusta da muke ciki ne aka cika shekara guda da dawowar kungiyar kan shugabancin kasar.

Kungiyar ta dawo kan mulki ne shekara 20 bayan sojojin kawancen Amurka sun hambarar da gwamantinta a shekarar 2001.

A shekarar 1996 Taliban ta kafa gwamnati a kasar bayan ta hambarar dag gwamnati mai ci a wancan lokaci.