Mijin Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka, Kamala Harris, wato Douglas Emhoff, ya tsallake rijiya da baya daga harin bom.
A ranar Talata ce, masu tsaron lafiyar Mista Emhoff, suka janye shi bayan baranazar harin bom da aka samu a wata makarantar sakandare mai suna Dunbar Highschool da ya ziyarta a birnin Washington DC.
- Ababen hawa na lalacewa bayan NNPC ta shigo da gurbataccen mai lita 100m
- Putin ya ce Rasha ba za ta ruruta wutar rikicin Ukraine ba —Macron
Ya ziyarci makarantar ce domin bikin zagayowar Ranar Tarihin Amurkawa ’Yan Asalin Afirka wanda ake gudanarwa a yayin bikin Watan Tarihin Bakar Fata.
Mai magana da yawun makarantun gwamnati a Washington DC, Enrique Gutierrez, ya shaida wa manema labarai cewa, “An samu barazanar harin bom a makarantar… shi ne muka dauki matakin kwashe kowa daga cikin ginin, kamar yadda kuka gani.”
Bayan janye Mista Emhoff ne aka umarci dalibai da sauran daukacin mutane su fice daga harabar makarantar.
Ya zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto, hukumomin Amurka ba su fitar da wani bayani dangane da irin barazanar harin bom din ake zargi ba.
Mijin Kamala Harris na nan lafiya
Mai magana da yawun Mista Emhoff, Katie Peters, ta ce, “An sanar da hukumar tara bayanai cewa akwai barazana a makarantar da @SecondGentleman yake ganawa da dalibai da kuma malamai.”
“Mista Emhoff yana cikin koshin lafiya kuma an fitar da kowa daga uwrin.
“Muna yin jinjina ga hukumar tara bayanai da ’yan sanda bisa wannan namjin kokari da suka yi,” inji sanarwar da ta fitar.
Mijin mataimakiyar shugaban kasa na farko
Kamala Harris ita ce mace ta farko kuma bakar fata ta farko da aka zaba a matsayin Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka.
Mijinta, Emhoff kuma, wanda lauya ne, shi ne wanda ya fara zama mijin mataimakiyar shugaban kasar.
Yana kuma yawan yin tafiye-tafiye shi kadai ko tare da matar tasa domin tallata manufofin fadar White House.