✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin bom din Boko Haram ya hallaka matafiya a Borno

Mutane da dama da sun salwana bayan bama-baman Boko Haram sun tashi da wasu manyan motoci a hanyar Maiduguri zuwa Damboa a Jihar Borno.

Mutane da dama da sun salwana bayan bama-baman Boko Haram sun tashi da wasu manyan motoci a hanyar Maiduguri zuwa Damboa a Jihar Borno.

Irin hadarin da ke kan hanyar da ta tashi daga Maiduguri ta bi ta Damboa zuwa Biu, ya sa tun farko sojoji suka rufe ta, kafin a baya-bayan nan su bude, bayan yanayin tsaron yankin ya kyautata.

Adamu Yahaya wanda ya tsallake rijiya da baya ya ce: “’Yan ta’addan sun far wa wasu manyan motocin da ke jigilar kayan abinci kana suka yi awon gaba da akasarin kayayyakin da suke dauke da su, suka gudu da su zuwa maboyarsu da ke Dajin Sambisa.”

Ya kara da cewa, maharan sun kona wasu gidaje tare da kwace kayan abinci da sauran kayayyakin amfani sannan suka tsere zuwa dajin Sambisa kamar yadda na fada.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a Maiduguri, Shugaban Karamar Hukumar Chibok, Umar Ibrahim, ya ce: “Wasu ’yan Boko Haram da ba a tantance adadinsu ba sun kai hari kauyen a safiyar ranar Litinin.”

A cewarsa, maharan sun yi ta harbe-harbe a iska tare da kashe mutanen kauyen uku kafin su kona wasu gidajen bayan da suka tayar da bama-bamai da suka lalata motoci biyu da ya kai halaka wasu mutane.

Babban Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai, Manjo-Janar Christopher Musa ya bukaci Gwamnatin tarayya da ta Jihar Borno su gyara hanyar Maiduguri-Biu saboda ’yan ta’addan na amfani da lalacewarta wajen yi wa matafiya da mazauna yankunan barna.

Ya ce munin hanyoyi na rura wutar rikicin Boko Haram tare da kawo tsaiko ga sojoji wajen kai dauki ga al’ummomin da ke neman dauki bayan an kai musu hari.

A cewarsa, sake gina hanyar Maiduguri-Biu, Maiduguri-Monguno da Maiduguri-Dikwa-Gambouru na iya hana ’yan ta’addar damar ia dasa bama-bamai a kan hanyoyin.