Wani harin bam da aka kai ranar Litinin kan wata motar ’yan sanda a wata kasuwar birnin Quetta na kasar Pakistan ya hallaka mutum hudu.
Hukumomin ’yan sandan kasar sun kuma ce baya ga wadanda suka rasu, mutanen da suka jikkata sun kai 15.
- ‘Yan sanda sun kashe mai garkuwa da mutane yana kokarin karbar kudin fansa
- Birtaniya ta dakatar da daukan ma’aikatan lafiya daga Najeriya
Kazalika, Kakakin wani asibiti da ke Quetta ya ce daga cikin wadanda suka mutun har da wata mace, sannan a cikin wadanda suka jikkata ma akwai mata biyu.
“Mutum hudu dun rasu, wasu 15 kuma sun jikkata,” in ji Kakakin.
Wani babban jami’in dan sandan kasar, Shafqat Cheema, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an yi kokarin kai harin ne kan motar wani babban dan sanda mai kula da bincike wacce ya ajiye a unguwar Kandahari Bazar.
Ya ce wani bincike ya nuna cewa an dasa wani abin fashewa ne a jikin wani babur da aka ajiye a bayan motar.
Daga cikin mutanen da suka mutu dai har da wasu ’yan sanda biyu da ke cikin motar, kamar yadda dan sanda mai kula da ayyuka, Zohaib Mohsin Baloch ya tabbatar.
Binciken farko-farko dai ya nuna an yi amfani da kilogiram hudu zuwa biyar na abin fashewar a jikin babur din, wanda kuma aka yi amfani da rimot wajen tayar da shi.
Wannan ne dai karo na biyu da ake kai wa ’yan sanda hari cikin sa’o’i 24.
Ko a yammacin Lahadi sai da aka kashe wasu ’yan sanda biyu sannan aka jikkata wani guda a wani hari, su kuma maharan aka kashe musu mutum daya.