Wani bam da aka tayar a cikin wata mota a tsakiyar lardin Ghazni na kasar Afghanistan ya kashe akalla jami’an tsaron kasar 30 a ranar Lahadi, kuma asarar rayuka na iya karuwa duba da yanayin wurin da bam din ya fashe.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Cikin Gida Tariq Arian ya tabbatar da cewa an samu fashewar bam a cikin mota amma bai bayar da wani karin bayani game da lamarin ba.
- Dalilin da ya sa muke sulhu da ‘yan bindiga – Gwamnatin Sakkwato
- ‘Ayyukan ta’addanci na karuwa a Kano’
Sai dai Baz Mohammad Hemat, darektan asibitin lardin Ghazni, ya ce an kai gawawwaki 30 da kuma mutane 24 da suka jikkata.
Fashewar bam din ta tarwatsa wani rukuni na sansanin jami’an tsaron jama’a da wasu yankin gidajen mutane da ke yankin, lamarin da ke nuna yiwuwar samun karin wanda suka mutu.
Sai dai ya zuwa yanzu babu wata kungiya ta ‘yan ta’adda da ta nuna alhaki a kan fashewar bam din.
A yayin da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya tuntubi Mai Magana da yawun kungiyar ‘Yan Taliban, Zabihullah Mujahid, bai tabbatar ko musanta alhakin hakan ba.
Kasar Afghanistan ta kai tsawon shekaru 20 tana fama da rikicin yake-yake tsakanin gwamnati da ‘yan Taliban, wanda kasashe da dama suka dinga shiga tsakani domin ganin an tsagaita wuta.