✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin bam a masallaci ya kashe mutum shida a Somaliya

Hukumomi a Somaliya sun tabbatar da mutuwar mutum shida bayan wani harin bam da aka kai a wajen wani masallacin Juma’a a birnin Kismayo. Rahotanni…

Hukumomi a Somaliya sun tabbatar da mutuwar mutum shida bayan wani harin bam da aka kai a wajen wani masallacin Juma’a a birnin Kismayo.

Rahotanni kuma sun ce ana fargabar akalla wasu mutum 20 sun samu munanan raunuka a harin da ake zargin an kai shi ne kan wani fitaccen dan siyasar yankin.

“Wani dan kunar bakin wake da ya yi damara da abubuwan fashewa ya kai hari a masallacin Juma’a na Qaadim a tsakiyar birnin a daidai lokacin da mutane ke kokarin fita bayan kammala sallar Juma’a”, inji Abdinnasir Gulled.

Birnin Kismayo dai na da matukar muhimmanci a Somaliya kasancewar shi yake dauke da babbar tashar jiragen ruwa ta kasar.

Tuni dai kungiyar Al-Shabaab ta bakin gidan rediyonta na Andulus ta dauki alhakin kai harin.

Kungiyar wacce ke da alaka da ta Al-Ka’ida na yawan kai hare-hare a kan jami’an gwamnati, ’yan jarida, fitattun ’yan kasuwa da kuma sauran mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kasar mai fama da rikici.