✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin bam a masallaci ya hallaka mutum 5 a Afghanistan

Wannan dai shi ne hari mafi girma a kasar tun bayan ficewar Amurka daga kasar.

Wani bam da ya fashe a kofar wani masallaci da ke birnin Kabul babban birnin Afghanistan ranar Lahadi ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar.

Kakakin Taliban, Zabihullah Mujahid ya tabbatar da kai harin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya ce wasu mutum hudu kuma sun jikkata.

Wannan dai shi ne hari mafi girma da aka kai a kasar tun bayan ficewar dakarun Amurka daga kasar a karshen watan Agusta.

An kai harin ne kusa da masallacin Eidgah da ke Kabul, a inda ake gudanar da wani taron tunawa da mahaifiyar kakakin na Taliban, Zabihullah.

Daga bisani dai kakakin ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa harin ya lakume rayuka da dama.

Kazalika, Taliban ta tabbatar da kama mutum uku da ake zargi da hannu a harin.

Sai dai ya ce fararen hula ne suka rasu, ba mayakan Taliban ba, ko da yake bai bayar da adadin wadanda suka mutun ba, inda ya ce ana ci gaba da bincike.

Wani asibitin bayar da agaji na kasar Italiya ya wallafa a shafin Twitter cewa ya karbi mutum hudu da suka ji rauni a harin.

Rahotanni sun ce jim kadan da kai harin, ’yan Taliban sun yi wa masallacin tsinke, sannan daga bisani aka wanke wajen kamar ma ba a kai harin ba, in ban da alamar wasu gilasai da suka farfashe a kofar masallacin.

Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Sai dai tun bayan karbar mulkin Taliban a tsakiyar watan Agusta, ana zargin kugiyar IS da zafafa kai hare-hare a kasar.

Rabon da a sami hari irin wannan harin tun lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tayar da wani bam dab da inda ake kwashe mutane a filin jirgin sama na Kabul, inda sama da mutum 169 suka mutu.