Kasashen duniya na yin Allah wadai da harin da sojojin Rasha suka kai kan wani asibitin yara da ke birnin Mariupol a kasar Ukraine, a ci gaba da luguden wutar da Rashar ke yi a mamayar da ta yi wa Ukraine.
Wannan kazamin hari a asibitin yana zuwa ne a daidai lokacin da Magajin Garin Mariupol, ya ce mutane sama da 1,200 sun mutu sakamakon lugudn wutar sojojin Rasha da suka kwashe kwanaki tara suna kai wa a Kudancin Ukraine.
- Real Madrid ta kora PSG gida; Man City ta tsallaka zagaye na gaba
- NAJERIYA A YAU: Yadda Rashin Wutar Lantarki Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Kunci
Yayin la’antar harin asibitin, Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya gabatar da wani bidiyo da ke nuna yadda aka ragargaza asibitin, inda ya ce harin na Rasha ya binne yara a ciki.
Daga cikin wadanda suka soki Rasha kan kai hari asibitin har da fadar White House ta Amurka da Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson da kakakin Majalisar Dinkin Duniya.
Ita kuwa Rasha ta zargi sojojin Ukraine da mayar da asibitoci cibiyoyin kaddamar da hare-hare, bayan sun kwashe marasa lafiya da jami’an da ke kula da su.
Yanzu haka dai ana ci gaba da laluben masu jinya da ake tunanin gini ya danne su, wanda aka fara tono wasu daga cikinsu.