Harim bom ya hallaka mutum 15 tare da jikkata wasu 30 a wani ginin gwamnati da ke Gabashin Afghanistan a ranar Asabar.
Gwamnan lardin Nangarhar, Attaullah Khogyani, ya ce maharan sun tayar da bom din da ke cikin wata mota ne a wani ginin sojoji a yankin Ghani Khel.
- COVID-19: Trump ya kwanta a gadon asibiti
- An gano yarinyar da fasto ya sace bayan shekara 7
- ‘Yadda na tsere daga hannun Boko Haram’
“An tayar da bom din ne a kofar shiga babban ofishin yankin inda maharan suka yi kokarin shiga cikin ginin amma jami’an tsaro suka karkashe su”, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Kakakin ’yan sandan lardin, Farid Khan, ya ce akasarin wadanda suka rasu jami’an tsaron kasar ne sai kuma wasu fararen hula.
Babu wanda ya dauki nauyin kai harin duk da cewa kakakin ’yan sandan ya zargi kungiyar Taliban, wadda ita da kungiyar IS kan kai hare-hare a yankin.
Sai dai kuma tun a watan Fabrairu aka fara kokarin cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Taliban da gwamnatin Afghanistan.
Yarjejeniyar wadda Amurka ke jagoranta a birnin Doha na kasar Qatar ta shardanta wa kungiyar dakatar da kai hare-hare.
A baya kungiyar ta nesanta kanta wasu hare-hare da aka kai a sassan Afghanistan, kasar da ta shafe shekara 20 tana fama da yake-yake.