Gwamnatin mulkin soji ta Burkina Faso na fuskantar tashin hankali mafi muni na masu jihadi bayan wasu hare-haren da ’yan ta’addar suka kai.
Wannan lamari dai ya ci gaba da ta’azzara tun bayan da sojojin suka karbi mulki a cikin watan Janairun da ya gabata.
- Yadda aka kama fasto ya yi wa karamar yarinya fyade
- Real Madrid ta tallafa wa yaran da yakin Ukraine ya mayar ’yan gudun hijira
Fararen hula 23 da jami’an tsaro 13 ne suka mutu a wasu jerin hare-hare guda hudu a cikin ’yan kwanakin nan a yankin Dori, daya daga cikin manyan garuruwan Arewa maso Gabashin kasar.
Gidan Rediyon Jamus ya ruwaito cewa wannan hari shi ne mafi muni tun bayan da Kanal Paul-Henri Sadaogo Damibaya karbe ragamar mulki a kasar.
A cikin watan Faibrairun da ya gabata ne Kanal Damiban ya hambarar da gwamnatin Shugaba Roch Marc Christian Kaboré a kan dalilan gaza magance matsalar rashin tsaro.