✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hare-hare 16 da ’yan bindiga suka kai cikin sati 2 a Arewa

Ba su raga wa garuwa da filin jirgi ba, balle kauyuka, gonaki, makarantu da gidajen yari.

A ’yan shekarun nan, ’yan bindiga sai kara addabar Arewacin Najeriya suke yi, suna hana al’ummar yankin rawar gaban hantsi.

Ba su raga wa garuruwa da filin jirgin sama ba, balle kauyuka, gonaki, makarantu, hanyoyi, kasuwanni da gidajen yari. A baya-bayan nan jihohin Filato da Taraba sun shiga shahun wuraren da ake yawan kai wadannan hare-hare.

’Yan ta’adda su yi wa mutane kisan gilla ko su sace su don karbar kudin fansa ba sabon abu ba ne a yankin.

Iyalai da masoya ba su da zabi face su su sayar da ’yan kadarorinsu su yi karo-karo su biya kudin fansa saboda a sako ’yan uwansu da aka yi garkuwa da su.

A baya-bayan nan abin ya kara muni, inda a mako biyu da suka gabata aka kai irin wadannan hare-hare akalla sau 16 a jihohin Zamfara, Kaduna, Neja, da Katsina kamar haka:

Filin jirgin saman Kaduna

A ranar Asabar, 26 ga Maris, 2022, ’yan bindiga aka babura su mamaye filin jirgin sama na Kaduna da misalin karfe 1:00 na rana.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar wani jami’in tsaro mai suna Shehu Na’Allah a kan titin jirgin gami da hana wani jirgi tashi zuwa Legas da misalin karfe 12:30 na dare.

Giwa: Harin Hayin Kanwa

Washegari, Lahadi, kuma aka kashe akalla mutum 15 a farmakin da ’yan bindiga suka kai kauyukan Hayin Kanwa da Unuguwar Yakawada da ke karamar hukumar Giwa ta jihar.

Kafin harin da kwana uku uku an kashe kimanin mutum 50 a wasu kauyuka tara na karamar hukumar, wadda ’yan bindiga ke yawan kai wa hari.

An sace fasto da mutum 44

A ranar Lahadin, ’yan bindiga suka yi garkuwa da Rabaran Leo Rapael Ozigi, limamin cocin Katolika na St Mary’s da ke Sarkin Pawa a Jihar Neja, da wasu mutum 44.

Rabaran Leo ya ci karo da ’yan bindigar ne a hanyarsa ta zuwa Gwada daga Sarkin Pawa, a jihar, inda suka tisa kayarsa tare da mutanen wani kauye da suka sace zuwa daji.

Matafiya a motar gwamnati

Ranar Talata, 29 ga watan Maris kuma aka sace wasu fasinjoji bakwai a motar hayar kamfanin sufuri na Benue Links, mallakin Gwamnatin Jihar Binuwai.

Mako guda kafin nan an yi garkuwa da wasu fasinjoji shida a motar kamfanin a Ochadamu, Jihar Kogi, a hanyarsu ta zuwa Legas, sai da aka biya kudin fansa kusan Naira miliyan 5 kafin aka sako su.

An kashe manoma a hanyar Abuja

Washegari kuma aka sace wasu manoma magidanta biyu a kauyen Unguwar Barde a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

An sace manoman ne a lokacin da suke aikin share gonakinsu a shirye-shiryen su na fara aikin noman damina. 

Harin Unguwar Bulus

Da misalin karfe 8 na dare ranar Alhamis, 31 ga Maris, mahara suka kutsa kauyukan Unguwar Bulus da Unguwar Gimbiya da ke Jihar Kaduna inda suka kwashe sa’o’i suna harbi kan mai tsautsayi, lamarin da ya sa yawancin mutane suka tsere.

Wani mazaunin garin ya shaida mana cewa maharan sun sace kawunsa wanda suka kashe dansa a lokacin harin na Unguwar Bulus.

’Yan bindiga sun mamaye hanyar Abuja

An samu labarin bullar dandazon ’yan bindiga da suka tare babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja suna harbe-harbe da misalin karfe 3 na rana, wanda hakan ya tilasta wa masu ababen hawa yin gaggawar juyowa.

Ba a samu labarin sace su ba, amma majiyoyi a kan babbar hanyar sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun bi ta wata unguwa mai suna kauyen Kwari da ke kusa da wurin.

Amma daga bisani Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida nai jihar Samuel Aruwan, ya karyata cewa ’yan bindiga ba su kai farmaki kan babbar hanyar.

Kauyuka 4 a Zamfara

Mahara sun kai farmaki a wasu kauyuka hudu inda suka yi wa mutum 17 kisan gilla rana tsaka a Karamar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara, ranar Juma’a, 1 ga Afrilu, 2022.

Mazauna sun ce ’yan bindigar sun shiga kauyen Kadaddaba da rana, suna ta harbe-harbe duk da cewa babu wata tsokana daga mazauna yankin da zai sa a kai harin.

’Yan bindiga sanye da ‘kakin soja’

’Yan binida sanye da kakin soja sun kutsa garin Tsafe, hedikwatar Karamar Hukumar Tsafe ta jihar, inda suka kashe mutum hudu ciki har da dan Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Mamman Tsafe a safiyar ranar 4 ga Afrilu, 2022.

Sabon hari a kauykan Neja

Shaidu sun tabbatar cewa da misalin karfe 5:00 na yamma ranar Alhamis, 7 ga Afrilu, aka far wa kauyen Daza da ke Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja lamarin da ya tilasta mutane barin gidajensu ganin yadda maharan dauke da manyan makamai ke cin karensu babu babbaka.

A ranar kuma, an kashe mutum uku, an jikkata wasu da dama, aka sace wasu da dama a wani hari a unguwar Rumache-Madalla da ke Bassa/Kukoki a Karamar Hukumar Shiroro ta jihar.

Gonar Gwamnatin Tarayya

Da sanyin safiyar Litinin 11 ga Afrilu, 2022, mahara suka far wa wata gona mallakin Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Kasa da ke garin Kujama a Jihar Kaduna suka kashe mutum daya suka sace shanu da wasu dabboi da ba tantance adadinsu ba.

Wani shugaban al’umma a Kujama, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa ya ce maharan sun yi awon gaba da kusan daukacin shanu da tumakin da ke gonar.

An kashe mutane 23, an sace wasu a Giwa

Washegari ’yan bindiga sun kashe mutum 23 suka  raunata wasu da dama a kauyukan Anguwar Maiwa da Anguwar Kanwa a Karamar Hukumar Giwa ta jihar. 

Wani ganau ya ce an gano gawarwaki 23 daga cikin mutum 23 da ’yan bindigar suka kashe a harin da suka kai da misalin karfe 1:00 na dare.

Harin shi ne na hudu a jere da ’yan bindiga suka kai cikin mako guda a kauyukan karamar hukumar.

An sace matar aure da ’ya’yan miji

An yi garkuwa da wata matar aure da ’ya’yanta guda uku a unguwar Jabiri da ke Karamar Hukumar Funtua a Jihar Katsina. 

’Yan bindigar sun kutsa daya daga cikin gidajen wani mai suna Shamsudeen Muhammad Kalgo da sanyin safiyar Talata suka tafi da matarsa ​​Malama Badiyya da ‘ya’yansa hudu.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, yayan magidancin ya ce kanin nasa yana wurin uwar gidarsa a wani gidan a lokacin da lamarin ya faru.

Daliban Kwalejin Lafiya a Zamfara

A ranar Laraba ma an sace wasu dalibai mata a Kwalejin Fasaha ta Lafiya ta Tsafe a Jihar Zamfara. 

Wani malami a makarantar, wanda ya yi nemi a sakaya sunasa ya ce masu garkuwar sun yi awon gaba da daliban ne daga dakin kwanansu da ke wajen harabar makarantar.

Ba a dai san ainihin adadin daliban da aka sace ba, amma wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa daliban da ’yan bindigar suka dauke za su kai mutum biyar.