✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harbin bindiga a fadar Olubadan ya haifar da takaddama

Harbe-harben bindiga da aka yi a fadar Olubadan na Ibadan a ranar Litinin da ta gabata ya haifar da takaddama tsakanin Gwamnan Jihar Oyo, Abiola…

Harbe-harben bindiga da aka yi a fadar Olubadan na Ibadan a ranar Litinin da ta gabata ya haifar da takaddama tsakanin Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi da ’yan siyasa, inda yake zargin cewa saboda sun kasa kai gaci ne ya sa suke kokarin shafa masa kashin kaji domin dawo da rikicin siyasa da kashe-kashen rayuka a Jihar Oyo.

Gwamnan ya roki Olubadan da ya daina mu’amala da irin wadannan ’yan siyasa masu kokarin mayar da hannun agogo baya.

Kwana daya bayan aukuwar lamarin ne gwamna ya yi wata ganawar gaugawa da kwamandojin rundunonin tsaro na soja da ’yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki, a inda suka tattauna a kan wannan al’amari. Haka kuma a Larabar da ta gabata, ya sake yin irin wannan ganawa da sarakuna da shugabannin al’umma daga kananan hukumomi 11 na masarautar Ibadan.

A ta bakin mai ba shi shawara a kan harkokin tsaro, Mista Segun Abolarinwa, gwamnan ya ce akwai wasu ’yan siyasa da ake zargin suna da hannu wajen tayar da zaune tsaye a kan batun daukaka darajar hakimai zuwa sarakuna a masarautar Ibadan da gwamnan ya yi kwanan baya.

’Yan bindigar da suka kai harin na ranar Litinin, sun yi harbe-harbe a iska ne domin tsoratar da daruruwan mutane da suka halarci bikin nada wasu hakimai da Olubadan, Oba Saliu Adetunji ya yi, a daidai wannan lokaci. Hakan ne yasa mutane tserewa daga fadar domin neman mafaka. Babu wanda ya rasa ransa kuma harsashin

bindiga bai taba jikin kowa ba amma mutane masu yawa sun samu raunuka a kokarin tsira da rayukansu. Wata mota kirar Toyota Land Cruiser mallakar tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Oyo Cif Sharafadeen Alli, tana daga cikin motoci 2 da harsashin bindiga ya lalata gilasansu.

Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Rasheed Ladoja wanda yake rike da sarautar Osi Olubadan da Sanata Femi Lanlehin da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Cif Sharfadeen Alli, suna daga cikin manyan mutanen da ke tare da Olubadan a cikin fadarsa a lokacin da al’amarin ya faru.

Jayayya a tsakanin Gwamna da Olubadan ta fara kunno kai ne kwanan baya, a lokacin da Gwamnan ya yi bikin mika sandar sarauta da satifiket ga hakimai 27 da aka daukaka darajarsu zuwa matsayin sarakuna a masarautar Ibadan. Olubadan bai halarci wajen bikin ba, domin nuna rashin amincewa da wannan al’amari. Ganin cewa da yawa daga cikin hakimansa sun goyi bayan batun daukaka darajarsu zuwa sarakuna sai Olubadan ya shirya nada sababbin hakimai da za su maye gurbinsu. A daidai lokacin da yake bikin nada sababbin hakiman nasa ne wannan al’amari ya auku, a inda ’yan bindigar suka tarwatsa taron.

Tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rasheed Ladoja ya ce dokar nadin sarautun gargajiya ta Jihar Oyo ta amince wa Olubadan yin wannan nadin, wanda bai amince ba sai ya je kotu a maimakon tayar da hankalin jama’a. Ya ce bai ga dalilin da ya sa Gwamna Abiola Ajimobi da ke kan gado yake daukar matakan tayar da zaune tsaye a maimakon samo hanyar kwantar da hankalin jama’a a masarautar Ibadan ba.

A Larabar da ta gabata, Mataimakin Sufeto Janar na ’yan sanda mai kula da shiyya ta 11, Agboola Oshodi-Glober ya ziyarci fadar Olubadan, inda ya bayar da tabbacin cewa za su yi duk abin da suke iyawa wajen gano ’yan bindigar da suka kai harin, domin su.