Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce hukuncin da Kotun Kolin Amurka ta yanke na haramta zubar da ciki a fadin kasar zai kawo wa duniya matukar koma-baya.
Shugaban hukumar, Dokta Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana hakan, inda ya ce hukuncin kawo karshen wannan dadaddiyar dokar koma-baya ne.
- An kashe fararen hula sama da 300,000 a rikicin Siriya — Rahoto
- Kotu ta soke belin wanda ake zargi da sassara dan makwabcinsa saboda kare
Akalla jihohin Amurka takwas sun riga sun dauki matakin haramta zubar da ciki sai dai in an jin tsoron cewa rayuwa za ta shiga hadari.
Ana kuma sa ran jihohi da dama a nan gaba za su shiga sahun dabbaka dokar kwanan nan.
Da yake zantawa da manema labarai a Geneva, Tedros ya yi gargadin cewa kasa mai tasiri kamar Amurka za ta fuskanci koma-baya na shekaru masu yawa kan batun.
Ya kara da cewa, “Muna fata Amurka ta zama jagora kan al’amarin.”
Kzalika, ya ce akwai yiwuwar kasashe da dama su yi koyi da Amurka wajen tabbatar da dokar, kana ya yi gargadin tasirin da hakan zai yi ga duniya da cewa abin damuwa ne.
Tedros ya dage kan cewa, “A bai wa mata ‘yancin yin ra’ayi idan aka zo batun da ya shafi jikkuna da kuma lafiyarsu.”
Bugu da kari, ya ce zubar da ciki bisa ka’ida hanya ce ta kula da lafiya da ceto rayuka.
Yayin da haramta zubar da cikin kan ingiza mata da ‘yan mata zuwa ga zubar da ciki ta hanya mai tattare da hadari wanda a wasu lokutan akan rasa rai.
A nata bangaren, babbar jami’a a hukumar WHO, Soumya Swaminathan ta ce bayar da damar zubar da ciki bisa ka’ida hanya ce ta ceton rayuwa.
Hana wannan damar kuwa “Tamkar hana mutane amfani da maganin da sukan cewa zai ceci rayuwarsu ne,” inji ta.