✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Har yarzu matata na soyayya da tsohon mijinta’

Miji ya gano matarsa tana soyayya da tsohon mijinta

Wani manomi ya shaida wa Kotun Kwastomari da ke zamanta Ibadan cewa ya kama matarsa tana mu’amalar soyayya da tsohon mijinta.

Magidancin ya bukaci kotun da ta datse igiyar aurensa da matar da suka kwashe shekara biyar tare wadda ya ce ta dauki dabi’ar yin shigar bayyana tsiraici.

“Matata na haduwa da tsohon mijinta a boye suna hirar soyayya.

“Tana da tsananin girman kai tare da karya umarnina da tsare-tsaren zamantakewar iyali da na sanya.

“Tana yin shigar banza,  ba ta yin lullubi sannan ta rantse cewa ba za ta rika yin salloli biyar na farilla ba.

“Suna kuma musayar sakonnin soyayya tsakaninta da tsohon mijin nata,” kamar yadda ya shaida wa kotun.

A nata bangaren, matar ta bayyana zargin da mijin nata ke mata a matsayin zuki ta malle.

“Mijin nata kasurgumin makaryaci ne saboda rabona da yin ido hudu da tsohon mijina an fi shekara 10, kuma babu abun da ke shiga tsakani na da shi,” inji matar.

Daga nan alkalin da ke sauraren karar, Mai shari’a Cif Ademola Odunade, ya raba auren nan take domin samar da zaman lafiya a tsakaninsu.

Alkalin ya ba da umarnin cewa matar ta ci gaba da kula da ’ya’ya biyu da suka haifa sannan mijin ya rika ba ta kudin kula da su N10,000 a kowane wata.