Wani mamba a kwamitin binciken zargin cin zalin jami’an ‘yan sanda a jihar Delta, Mista Harrison Gwamnishu ya bayyana takaicinsa cewa har yanzu jami’an tsaro ba su koyi darasi daga zanga-zangar #EndSARS da ta tsayar da abubuwa cik a Najeriya na kusan kwanaki 10 ba.
Harrison wanda daya ne daga cikin ‘yan gaba dai gaba dai wajen ganin an yi wa harkar aikin ‘yan sanda kwaskwarima ya bayyana haka ne Asaba babban birnin jihar Delta yayin kaddamar da zaman kwamitin.
- Matakin da ya kamata Buhari ya dauka kan masu zanga-zangar #EndSARS
- An cafke ‘barayi’ 238 da taraktoci 35 a Adamawa
Ya ce yanzu haka jami’an ‘yan sandan sun dukufa kama mutanen da ba su ji ba basu gani ba suna baje-kolinsu a matsayin bata-gari, tare da zarginsu da satar kayan jama’a da kuma aikata kisan kai.
A cewarsa, “Wannan ba abinda za mu lamunta ba ne. An zo an dauke wani tela a Asaba, yanzu haka an sama masa matsuguni a gidan yarin Ogwashi Uku tare da jefa matarsa mai cikin wata takwas cikin halin ni-‘ya-su.
“Kazalika daga aiken wani mai gadi sayo mai yanzu an kama shi bisa zargin sata da kisan kai.
“Lokacin da ake tsaka da zanga-zanga da satar kayan jama’a, ba mu ga ‘yan sanda suna kama mutane ba. Bayan kwana biyu kuma ka fara kama mutane bisa zargin sata da kisan kai a kan laifin da aka yi kwanaki biyu kafin kamen nasu,” inji Harrison.
Daga nan sai ya yi kira ga kungiyoyi masu zamna kansu, Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa (NUJ) da Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) a jihar ta Delta da su binciki tare da kai rahoton duk wani rashin adalci da ke da alaka da zanga-zangar.
Jihar Delta dai na daya daga cikin jihohin da zanga-zangar wacce ta rikide zuwa tarzoma ta yi wa mummunar illa wacce ta kai ga asarar rayuka da dukiyoyi da dama.