Fira Ministan Iraqi, Mohammed Shia al-Sudani, ya kare ci gaba da zaman sojojin Amurka a kasarsa, inda ya ce har yanzu ana bukatarsu wajen yaki da ISIS.
Ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da jaridar Wall Street Journal ta Amurka ta farko, wacce ita ce irinta ta farko tun bayan darewarsa kujerar a watan Oktoban bara.
- Shin da gaske cin wake ga mace mai juna biyu yana sa jariri ya yi kato sosai?
- Buhari zai karbo ‘kyautar zaman lafiya’ a Mauritaniya
Sai dai matsayin nasa ya ci karo da na kungiyoyin kasar da mabiya Shi’a ke da rinjaye a ciki, wadanda kuma su ne suka nada shi Fira Ministan a bara.
A tattaunawar da jaridar ta wallafa ranar Lahadi, Fira Ministan bai ba da wani takamaiman wa’adin da dakarun Amurka da na kungiyar kawance ta NATO za su bar kasar ba, duk da kiraye-kirayen yin hakan da suka yi yawa a kasar.
“Muna tunanin har yanzu muna bukatar dakarun na waje a kasarmu. Ganin bayan ISIS na bukatar karin lokaci,” in ji shi.
Amurka dai ta mamaye Iraqi ne tun a shekarar 2003, inda ta jibge dakarun da adadinsu ya taba kaiwa 170,000 a shekara ta 2007.
Sai dai daga bisani an janye su a shekarar 2011, amma aka sake dawo da su a 2014, bayan ISIS ta zafafa kau hare-hare.