Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi ya ce har yanzu hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ba ta biya shi basussukan albashin da yake bin ta bashi ba tun bayan da ta sallame shi daga kocin kungiyar a bara.
Keshi ya kara da cewa ba shi kadai abin ya shafa ba, har da masu taimaka masa a lokacin da yake horar da kungiyar, su ma ba a biya su albashin da suke bi bashi ba.
Kocin ya ce duk da yake ya yi rashin matarsa kimanin makwanni uku da suka wuce ya kusa dawowa harkar horarwa a kungiyar kwallon kafar da bai ambata ba. Ya furta wadannan kalamai ne a lokacin da yake hira da kafar sadarwar intanet ta thecable.ng a ranar Talatar da ta wuce.
Da aka tambaye shi ko zai sake horar da kungiyar Super Eagles idan aka sake yi masa tayi, sai ya amsa da cewa komai zai iya faruwa.
Sai dai ya nuna cewa da wuya hukumar NFF ta sake tuntubarsa game da horar da kungiyar Super Eagles saboda yadda ta kulla yarjejeniya da Sunday Oliseh kuma alamu sun nuna Oliseh yana iya bakin kokarinsa.
Stephen Keshi dai ya raba gari da Hukumar NFF ne a bara inda ta sallame shi kuma ta maye gurbinsa da Sunday Oliseh. Tun a wancan lokaci ne Keshi ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya kai hukumar kara gaban kotu saboda ba ta biya shi hakkokinsa ba kafin ta sallame shi.
Har yanzu NFF ba ta biya ni albashin da nake bi bashi ba – Stephen Keshi
Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi ya ce har yanzu hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ba ta biya…