✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu Najeriya rarrafe take ta fuskar ci gaba — Tinubu

Jamus ta ce za ta kulla alakar cinikayya da Najeriya ta ba ni gishiri in ba ka manda.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa har yanzu Najeriya rarrafe take ta fuskar ci gaba, amma gwamnatinsa ta dauki aniyyar sauya wa lamarin akala ta hanyar jagoranci na gari.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wannan Lahadin, yayin zantawa da Shugaban Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz da tawagarsa a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Shugaban ya kuma yi kiran da a inganta hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Jamus musamman a fannin tsaro, albarkatun kasa, ilimi, demokradiyya da sauransu.

Shugaba Tinubu, wanda ya ce hukuncin tabbatar da zabensa da Kotun Koli ta yi a makon jiya, ya sanya a yanzu ya mayar da hankalinsa ne kacokam kan ciyar da kasar gaba.

Ya ce yana maraba da inganta hadin gwiwa tsakanin Najeriya da gwamnatin Jamus ta fannoni da dama.

“Har yanzu Najeriya rarrafe take yi, amma mun kuduri aniyar ganin an sauya salo da samar da gwamnatin da za ta kawo sauyi a kasar,” in ji shugaba Tinubu.

A nasa jawabin, Shugaban Gwamnatin Jamus Scholz, ta jaddada bukatar kara inganta hadin gwiwa kan ababen more rayuwa, musamman a bangaren wutar lantarki da makamashi.

Kazalika, ya yi wa shugaba Tinubu godiya kan rawar da ya taka a kungiyar ta Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS), inda ya yi kira da a hada kai wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka da ma duniya baki daya.

Za mu fara sayen iskar gas daga Najeriya — Scholz

Olaf Scholz ya bayyana aniyar fara sayo iskar gas daga Najeriya da nufin cike gibin makamashi da kasarsa ke fama shi tun bayan raba gari da Rasha sakamakon mamaye Ukraine da ta yi.

A gabanin fara wata ziyarar aiki a Abuja da Legas da Accra, Scholz ya bayyana wa kafar yada labaran Daily Punch cewar kamfanonin gas na kasar Jamus na duba yiwuwar kulla alakar kasuwanci da Najeriya.

Scholz wanda ya yaba dimbin arzikin makamashin gas da Najeriya ke da shi, yana duba yiwuwar hada gwiwa da fadar mulki ta Abuja wajen bullo da wata sabuwar hanya samun sinadarin hydrogen.

Jagoran na Jamus na son kulla alaka mai karfi da tarayyar Najeriya a wani abin da ya kira bani gishiri in baka manda a tsakaninsu.

Wannan shi ne karo na 3 da shugaban gwamnatin Jamus ke kai ziyara a kasashen Afirka a kokarin fadada alakar kasarsa tun bayan darewa madafun iko kasa da shekaru biyun da suka gabata.

Bayan ganawa da mahukuntan na Najeriya shugaban gwamnatin Jamus Sholz zai je Lagos kafin ya karasa Ghana inda a can ma zai tattauna batuwan cinikayya a tsakanin kasashen.