✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu muna bincike don gano Manjo Janar Alkali – Rundunar Sojoji

Rundunar Sojojin Najeriya ta ce har yanzu jami’anta suna ci gaba da aikin janye ruwan wani kududdufi da ake zargin an jefa motar tsohon Jami’in…

Rundunar Sojojin Najeriya ta ce har yanzu jami’anta suna ci gaba da aikin janye ruwan wani kududdufi da ake zargin an jefa motar tsohon Jami’in Gudanarwa na Sojojin Najeriya, Manjo Janar Mohammed Idris Alkali.

Manjo Janar Alkali dai ya bace ne a ranar 3 ga Satumba, 2018 a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja.

Manjo Janar Alkali wanda ya yi ritaya daga aiki a watannin baya, an daina jin duriyarsa Ce a lokacin da yake tuka wata bakar mota kirar Corolla mai dauke da lamba MUN 670 AA.

Wata majiya daga Hedkwatar Tsaro ta Najeriya ta ce ya yi magana ta karshe a waya ne a wani yanki da ke karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

Bayanan sirrin da aka samu sun nuna cewa an jefa motar Janar Alkali a wani kududdufi da ke yankin Lafendeg da ke Gundumar Du a karamar Hukumar Jos ta Kudu, karamar hukumar da tsohon Gwamnan Jihar Filato, Jonah Jang ya fito.

Mataimakin Babban Kakakin  Runduna Soji ta uku da ke Rukuba a Jos Jihar Filato, Kanar Kayode Ogunsanya ya ce an shafe kwanaki fiye da biyar ke nan wajen aikin janye ruwan kududdufin da ake zargin an jefa motar Janar Alkali, amma kawo yanzu ba a kai ga gano komai ba.

Ya kara da cewa tun bayan marufin kofar wata farar bas mai daukar mutum 18 da aka samu a cikin kududdufin ba a kara gano komai ba.

A lokacin da Aminiya ta tuntubi  Kakakin Rundunar Musamman ta Tabbatar da Zaman Lafiya a Jihar Filato, (OPSH), Manjo Adam Umar ya ce dalilin da ya sa ba a kai ga janye ruwan ba shi ne kududdufin yana da zurfin gaske.

Ya ce, “Kududdufin yana da zurfi, a zahirin gaskiya ma babu wanda ya isa ya ce ga zurfinsa, amma ana ci gaba da janye kududdufin, kuma ba za a tsaya ba sai an tabbatar da an janyen ruwan da ke cikin kududdufin, don a gano abubuwan da suke cikinsa. Za mu gano ko motar Manjo Janar Alkali tana ciki ko a’a.”

Manjo Umar ya bayyana cewa jami’an da suke aikin yashe kududdufin sun hada da jami’an ba da agajin gaggawa daga Rundunar Soji ta Uku da jami’an rundunar tsaro ta OPSH da kuma ta rundunar ’yan sandan Najeriya da jami’an bIO da ’yan kwana-kwana da kuma masu ninkaya don ganin cewa batun janye ruwan bai samu tsaiko ba.

Idan ba a manta ba a lokacin da za a fara janye ruwan kududdufin wadansu mata daga Gundumar Du sun gudanar da zanga don ganin ba a janyen ruwan ba.

Ya ce, “Mun riga mun yi magana da wakilan matan tun a rana ta farko da za a fara janye ruwan, sun gamsu da aikin da za mu yi, don haka tun daga ranar ba su kara dawowa ba.”

Wata majiya da ke kusa da rundunar tsaro ta OPSH ta bayyana cewa a yanzu rundunar sojojin Najeriya ta kawo wadansu injinan janye ruwa daga Jihar Taraba duk don ganin aikin ya gudana ba tare da samun tsaiko ba. Manjo Umar ya bayyana cewa za su ci gaba da amfani da kafafen watsa labarai wajen bayyana wa jama’a yadda aikin yake gudana.