Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheik Ahmed Gumi ya tsaya kai da fata cewa matukar za a yi wa wadanda suka assasa yakin basasan da ya yi sanadiyyar mutuwar miliyoyin mutane, bai ga dalilin da zai sa a ki yin hakan ga ’yan bindiga ba.
Ya ce yin afuwar ya zama wajibi matukar Najeriya da gaske take yi wajen ganin ta kawo karshen matsalar tsaro.
- Rikicin Sasa: Kotu ta bada umarnin tsare mutum bakwai
- Yadda ’yan talla ke shiga karuwanci a Kano —Hisba
Malamin, wanda a kwanakin nan yake ta yunkurin ganin an gano bakin zaren kan kalubalen na tsaro na jaddada wadannan kalaman ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis yayin da yake mayar da martani ga Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) kan wasu kalamai da ta yi a kansa.
Ya ce, “Ban ga dalilin da zai hana a karbi tubansu a yi musu afuwa ba. Kun tambayi me zai sa a yi musu afuwa amma sun ce suna so su ajiye makamansu, sai dai suna tsoron bita-da-kullin shari’a daga bisani.
“Idan har kasar nan za ta iya yafewa masu yunkurin juyin mulki wadanda suka aikata laifukan cin amanar kasa zamanin mulkin soja, ina ganin babu laifi idan ’yan bindiga sun ci gajiya makamanciyar wannan afuwar a zamanin mulkin Dimokradiyya,” inji Sheik Gumi.
Malamin ya kuma ce sam kungiyar CAN ba ta fahimce shi ba saboda hatta bidiyon tattaunawarsa da ’yan bindigar da ya karade gari jirkita shi aka yi daga ainihin sakon da yake kunshe a cikinsa.
“Mun gano tushen matsalar kuma Gwamnatin Tarayya ce za ta iya yi musu afuwar. Abin mamakin shine suma mun gano wannan rikicin ya yi matukar shafarsu. Ana yi musu kudin goro. Ana kama da dama daga cikinsu a hukunta saboda kawai sun yi kama da makiyaya.
“Kamata ya yi ’yan Najeriya su rungumi juna su zauna lafiya, bai kamata mu yi abin da zai tayar da zaune tsaye ba. Ya kamata ’yan jarida suma su rika kaffa-kaffa kan abubuwan da suke fadi saboda kasar nan ta riga ta kama da wuta.
“Ku yi taka-tsan-tsan da abubuwan da kuke kawo rahotonsu. Ku ci gaba da aikinku da sanin ya kamata, ba wai rura wutar rikici tsakaninmu da ’yan uwanmu Kiristoci wadanda aka san su da son zaman lafiya ba. Mun jima a tare, babu wanda zai iya raba mu, don haka ya kamata mu koyi zaman lafiya da juna.”