Fadar Shugaban Kasa a ranar Talata ta caccaki babbar jam’iyyar adawa ta PDP saboda abin da ta kira da yin murna da labarin karya kan jifan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Jihar Kano.
A cewar Kakakin Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu a cikin wata sanarwa ranar Talata, har yanzu Buhari na da farin jininsa a Kano.
- DAGA LARABA: Dalilin Da Mutane Ke Karya
- Hadimar Gwamnan Sakkwato ta rasu sakamakon turmutsutsu a taron PDP
A ranar Litinin ce dai Sakataren Watsa Labarai na PDP na Kasa, Debo Ologunagba, ya yi Allah wadai da hare-haren da ya yi zargin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ne ya dauki nauyinsu don a kai wa Buharin a Kano, lokacin da ya je bude wasu ayyuka.
To sai dai a cewar Garba Shehu, salon adawar da PDP ta dauka na kokarin hada Buhari da Tinubu, ba zai fissheta ba a zabe mai zuwa.
Ya ce sabanin abin da ake ta yadawa, har yanzu Buhari na nan da farin jinin da aka san shi da shi a Kano.
“Masu jifa da duwatsun da aka gani a bidiyo suna fada da ’yan KAROTA, wasu yara ne da ba su ma san me yake musu ciwo ba da wasu gurbatattun ’yan siyasa da masu daure wa ta’addanci gindi suka dauki nauyi.
“Tayar da zaune tsaye da tarzoma ba su da muhalli a tsarin Dimokuradiyya.
“Ya kamata PDP ta yi amfani da yakin neman zabe wajen fada wa jama’a abin da za ta yi musu. Idan za a iya magance matsala cikin ruwan sanyi, babu bukatar jifa da ta da zaune tsaye, kamar yadda muke gani a wasu wuraren yakin neman zaben,” in ji Garba Shehu.
Ya kuma ce aiki shugabannin al’umma ne a kowanne mataki da malaman addini su tashi tsaye wajen fadakar da matasa illar ta da fitina saboda za ta cutar da su a nan gaba.
A ranar Litinin ce wasu hotuna da bidiyo suka bulla suna nuna matasa dauke da duwatsu na kokarin jifan jirgin saman da Shugaba Buhari yake ciki yayin ziyarar yini dayan da ya kai Jihar don bude wasu ayyuka.