✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu Faransa tana yi wa Afirka mulkin mallaka – Italiya

Faransa ta gayyaci Jakadiyar Italiya Faransa ta kira Jakadiyar Italiya a kasar bayan  da Mataimakin Firayi Ministan Italiya Mista Luigi di Maio ya zargi Faransa…

  • Faransa ta gayyaci Jakadiyar Italiya

Faransa ta kira Jakadiyar Italiya a kasar bayan  da Mataimakin Firayi Ministan Italiya Mista Luigi di Maio ya zargi Faransa da ci da gumin Afirka tare da kara rura kwararar ’yan ci-rani.

Mista Luigi di Maio ya yi kira ga Tarayyar Turai ta kakaba takunkumi ga Faransa saboda manufofinta a Afirka, musamman  irin yadda take ci gaba da mulkin mallaka a yankin.

Luigi ya ce, “Har yanzu Faransa ba ta daina mullkin mallaka ba a kan kasashen Afirka10.”

“Kasashen Turai ne suka sa mutane yin kaura, musamman Faransa wadda har yanzu ba ta daina yi wa kasashen Afirka mulkin mallaka ba,” in ji shi.

Ya ce ba domin Afirka ba, da yanzu Faransa tana matsayi na 15 a jerin kasashe masu karfin tattalin arziki maimakon na shida a duniya, inda ya zargi tattalin arzikin Faransa da ci-da-gumin wasu kasashen Afirka ta hanyar amfani da kudinta na CFA kamar yadda BBC ya ruwaito.

Wannan ne ya sa ofishin harakokin wajen Faransa ya kira Jakadiyar Italiya a Paris, Teresa Castald domin mika kokensa da kuma jin karin bayani.

Gwamnatin Italiya ta yanzu dai ta sha yin cacar-baki da kasar Faransa kan ’yan ci-rani da zanga-zanga da kuma al’adu.

Dangantaka a tsakanin Faransa da Italiya ta kara tsami ne tun kafa sabuwar gwamnatin Italiya a bara.

Kuma dangantar ta fi tsami ne kan batun ’yan ci-rani. Kuma kasashen biyu na jayayya ne kan yadda Faransa ke taso keyar ’yan ci-rani zuwa kan iyakar Italiya.

Italiya ta zargi Faransa da kin karbar ’yan ci-rani, bayan Faransa ta ce Italiya ba ta taimaka wa masu aikin ceto ’yan ci-ranin a teku.

A makon jiya ne ’yan ci-rani 2 suka rasu inda aka kubutar da 332 a gabar tekun Libiya.

Dakarun tsaron ruwa masu alaka da Gwamnatin Hadin Kan Kasa ta Libiya sun ce a cikin kwana 2 sun kai farmakai har sau 4 a tekun kasar inda suka kubutar da mutum 332 kamar yadda TRT ta ruwaito.

Sanarwar ta kara da cewa wadansu ’yan ci-rani ba bisa ka’ida ba su 2 sun mutu sakamakon zama a cikin teku mai sanyi har tsawon awa 24.

Ba a fadi ko daga wadanne kasashe mutanen suka fito ba.

Sakamakon matsalolin tattalin arziki da rikicin da ake yi a Libiya ’yan kasashen Afirka da ke son zuwa Turai na bi ta kasar inda a mafi yawancin lokuta suke rasa rayukansu a cikin teku ko fadawa hannun masu fataucin mutane.