Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya yi zargin cewa akwai yiwuwar nakasun fahimta ko kuma rashin samun sahihan bayanai game da sha’anin matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewacin Najeriya a tattare da takwaransa na Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai.
Ganduje ya ce ta yiwu El-Rufai bai fahimci matsalar tsaro da take addabar yankin Arewacin kasar ba, ko kuma ba ya samun bayanai na hakika game da matsalar.
- Dole sai mun yi sulhu da ’yan bindiga za a samu zaman lafiya — Matawalle
- A lalubi watan Rajab daga daren Juma’a — Sarkin Musulmi
- Farfesan Jami’ar Tafawa Balewa ya kubuta daga hannun ’yan bindiga
A wata hira da Gwamna El-Rufai ya yi da BBC, ya ce rashin hadin gwiwa dangane da yadda za a tunkari matsalar ta’addancin ’yan bindiga ita ce take kara ruwa wutar lamarin.
Sai dai a wata hira da ya yi da gidan Rediyon Faransa RFI, Gwamna Ganduje ya ce sun taba tattaunawa da El-Rufai da kuma Gwamnan Bauchi a kan yadda za a shawo kan matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya.
A cewar Ganduje, shi ne ya fara gabatar da batun matsalar tsaro a yayin tattaunawarsa da takwarorinsa, inda ya ankarar da su kan yadda za a samar da aminci a Dajin Falgore da ke Jihar Kano domin cin moriyar wasu Jihohin bisa shawarwarin da jami’an tsaro suka gabatar.
Ya ce gwamnatocin Bauchi da Kduna sun tura wakilai a wani taro da aka tattauna batun matsalar rashin tsaro da dabarun yadda za a maganceta, lamarin da a yanzu yake mamakin inda furucin Gwamna El-Rufai ya samo tushe na cewa akwai rashin hadin kai a tsakaninsu.
“Da farko, batun rashin hadin kai a tsakaninmu, ban san daga ina wannan magana ta samo asali ba, domin kuwa jami’an tsaro sun bamu shawarar cewa, Jihar Kano da Kaduna da Bauchi su tura wakilai zuwa Kano domin a tattauna a kan yadda za a magance matsalar ta’addanci a dajin Falgore da ya zama maboya ta ’yan bindiga.”
“Na tattauna da gwamnonin Kaduna da Bauchi kuma sun tura wakilai wanda kowace Jiha ta bayar da gudunmuwar kayan aiki har aka samu nasara, saboda haka inda dalilin furucin rashin hadin kai da El-Rufai ya yi.”
“Ni a nawa ganin, har yanzu El-Rufai bai yi wa lamarin kyakkyawar fahimta ba, don saboda kowane kalubale na matsalar tsaro ya kebanta da waninsa, kuma duk hadin kan da za mu yi, sai an samu banbanci kan yadda za mu tunkari matsalar.”
“A jihar Kaduna, akwai matsaloli na rikicin kabilanci da na addini, kuma wannan shi ne kalubalen da Jihar take fuskanta domin kowace jiha tana da nata kalubalen wanda kuma hakan ya ta’allaka ne da irin kokarin da Jihar take yi da jami’an tsaro wajen shawo kan matsalar a tsakanin al’ummarta.
“Misali a nan Jihar Kano, muna da kyakkyawar fahimtar juna a tsakaninmu da jami’an tsaro, inda a halin yanzu muke gina gidaje a dajin Dansoshiya domin samar wa Fulani makiyaya muhalli a kokarin da muke yi na ganin sun daina kora shanu kiwo zuwa Kudancin Kasar nan.”
GwamnaGanduje ya kuma yi tsokaci a kan yadda bakin makiyaya daga ketare suka shigowa kasar nan, lamarin da ya ce hakan na kara rura wutar matsalar rashin tsaro a kasar.
Kazalika, ya nemi a haramta wa Fulani makiyaya kora shanunsu kiwo daga Arewa zuwa Kudancin kasar wanda a cewarsa akwai wadataccen wurin da mikiyayan za su kiwaci shanunsu a dazukan Falgore da na Dansoshiya.