Har yanzu ragowar dalibai 17 na Jami’ar Greenfield ta Jihar Kaduna da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su fiye da tsawon kwanaki talatin da suka gabata, na ci gaba da zama a hannunsu ba tare da sanin halin da suke ciki ba.
Ana iya tuna cewa, da misalin karfe 8:15 na daren ranar 20 ga watan Afrilun da ya gabata ne aka sace daliban a kauyen Kakumi da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
- Mai Shari’a Adamu Bello ya zama sabon Hakimin Kankara
- Mahara sun kashe ’yan banga 19 a kauyen Sakkwato
Rahotanni sun bayyana cewa, an yi garkuwa da dalibai 22 ne yayin da kuma wani ma’aikacin jami’ar ya rasa ransa.
Daga bisa ni ne ’yan bindigar suk bukaci naira miliyan 800 a matsayin kudin fansar dalibai, inda bayan kwana daya da sace su aka samu gawar biyar daga cikinsu yashe kusa da jami’ar.
A yayin tattaunawarsa da Sashen Hausa na Rediyon Amurka, Shugaban ’yan bindigar mai suna Sani Idris Jalingo, wanda ake yi wa lakabi da ‘Beleri’, ya yi barazanar kashe ragowar daliban da suka rage a hannunsu muddin gwamnati ko iyayen daliban ba su biya naira miliyan 100 da motoci 10 kirar Honda da babura a matsayin fansarsu ba.
Tuni dai wa’adin biyan kundin fansar daliban ya cika, wanda kawo yanzu ba a ji wani bayani ko labarin halin da suke ciki ba.
Sai dai Kakakin ’Yan Sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya shaida wa Aminiya cewa rundunarsu na yin iya bakin kokarint wajen kubutar da daliban.
A cewarsa, “rundunar ’yan sandan jihar ba ta mance da daliban ba saboda Kwamishinan ’Yan sandan ya ba da umarnin kara kaimi wajen kubutar da su.”
Gwamnan Jihar Mallam Nasir El-Rufai na nan a kan bakansa tare da hawa kujerar naki ta biyan kudin fansa ga ’yan bindiga a jihar.