Shugaban Amurka Joe Biden ya ce har yanzu bai yanke shawarar ko zai tafi Saudiyya ba, mako guda bayan da bayyana yiwuwar yin bulaguro.
Majiyoyi sun ce Biden na shirin tafiya Saudiyya, daga nan ya wuce Turai da Isra’ila a karshen watan Yuni.
- Barcelona za ta kece raini da Madrid da Juventus a wasannin sada zumunta
- ‘Matsafa na bin makabartu su hako gawarwakin ’yan uwanmu’
Fadar White House ta ce shugaban kasar yana jin cewa Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, “ba ya bin doka.”
Bayanai sun ce Biden na yi wa Yariman wannan gani-gani saboda zarginsa da taka rawa wajen kisan dan jaridar Washington Post, Jamal Khashoggi, a Turkiyya a shekarar 2018.
Idan ba a manta ba, a shekarar 2018 ne Majalisar Dattawan Amurka ta dauki wani irin mataki da ba ta taba dauka ba kan kasar Saudiyya, kawar Amurka ta kud-da-kud, bayan da ta amince da wani kuduri na kawo karshen goyon bayan da Amurka ke bai wa Masarautar Saudiyya don yin Allah wadai da kashe Jamal Khashoggi.