✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu ban fidda ran kulob din Giwa zai lashe gasar Firimiya ba – El-Shittu

Duk da cewar alamu sun nuna zai yi matukar wahala kulob din Giwa FC da ke garin Jos a Jihar Filato ya iya rikito da…

Duk da cewar alamu sun nuna zai yi matukar wahala kulob din Giwa FC da ke garin Jos a Jihar Filato ya iya rikito da kulob din Enyimba da ke garin Aba a Jihar Abiya daga jagorancin gasar firimiya ta bana ta Najeriya, amma dan wasan baya na kulob din Giwa, Lawal El-Shittu ya bayyana har yanzu bai fitar da ran cewa kulob dinsa zai lashe gasar ta bana ba.
A yanzu dai Giwa na matsayi na hudu ne da maki 54 daidai da kulob din Wikki Tourist na Jihar Bauchi, inda kulob din Enyimba ya ba shi maki 7 saura wasanni 5 a kammala gasar ta bana, amma dan wasan ya bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa wajen ganin sun lashe gasar ba.
El-Shittu wanda ya jefa kwallon da ta sanya kulob dinsa ya samu nasara a kan Dolphins a lokacin da suka buga wasa a filin wasa na Rwang Pam da ke garin Jos a ranar Lahadi, ya bukaci ’yan wasan kulob dinsa su mayar da hankali, sannan su jajirce wajen ganin sun cimma burinsu na lashe gasar ta bana da kuma samo tikitin buga Gasar Zakarun Afirka a badi.
 “Muna sane da kalubalen da ke kanmu  a yanzu da wasanni biyar kacal suka rage a gasar ta bana, za mu je wa El-Kanemi Warriors da Heartland da kuma Nasarawa United wasa a waje, dukkan wadannan kulob suna fuskantar barazanar za a iya buga gasar badi ba tare da su ba, don haka muna sane da cewar za su yi yaki don ganin sun ci gaba da buga gasar a badi. Za mu buga wasa Wikki Tourist a nan Jos, kulob din Wikki na da karfi a baya da kuma gaba, a yanzu muna shirye-shiryen yadda za mu kara da wadannan kulob-kulob don ganin mun cimma burinmu.”
“Ina so in yi amfani da wannan damar wajen kira ga ’yan wasanmu da mu tashi tsaye, sannan mu jajirce wajen ganin mun lashe gasar ta bana, mun kuma samo tikitin buga gasar Zakarun Afirka a badi a nan garin Jos.” Inji shi.
dan wasan ya kuma roki ’yan kallo da su guji tayar da rikici yayin da ake buga wasa, sannan su karfafa musu gwiwa a lokacin da suke wasa a gida, musamman ma a wasansu da kulob din Wikki Tourist.