Wani ayarin Kwararru daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da ke bincike kan asalin cutar Coronavirus a China, ya ce har yanzu bai iya tantance ko daga dabbobi cutar ta samo asali ba ko daga dakin gwaje-gwajen kimiyya a China.
Wani kwararre kan abinci da dabbobi na Hukumar WHO, Peter Ben Embarek ya bayyana haka a ranar Talata a karshen ziyarar da suka kai birnin Wuhan da ke tsakiyar China inda ayarin masana kimiyya ke binciken asalin cutar ta COVID-19.
- Kotun Musulunci ta sa a kamo mawaki Rarara kan ‘boye matar aure’
- ‘2023: Arewa za mu sake ba takarar Shugaban Kasa a PDP’
An samu mutanen da suka fara kamuwa da cutar a birnin a watan Disamban 2019.
“Sakamakon farko na bincikenmu ya nuna akwai yiwuwar cutar ta faro ne ta hanyar wani abu da ya dauko ta daga tushenta zuwa yada ta – wannan ne abu mafi karfi zuwa yanzu kuma akwai bukatar a fadada bincike a kai,” inji Embarek.
“Sakamakon ya nuna abubuwan da suka faru a dakin gwaje-gwaje na matukar wahala a ce su ne musababbin yaduwarta ga dan Adam,” inji Embarek.
Cibiyar Nazarin Cututtuka ta Wuhan ta tattara samfuri da dama na kwayar cutar, wanda hakan ya sanya ake zargin cibiyar ce ta haddasa yaduwar cutar ta hanyar sakacin watsa cutar a cikin al’ummar da ke kusa.
Sai dai China ta sha musanta wannan zargi sannan ta yi ta yada wasu bayanan da ke nuna cewa watakila cutar ta samo asali daga wani wajen na daban ciki har da Amurka.
Ayarin na duba wasu bayanai da dama da kan yaya cutar ta fado ko ta kare a kan xdn Adam.
Liang Wannian kwararre a Hukumar Lafiya ta China ya fada wa manema labarai da ayarin na Hukumar WHO a Wuhan, cewa ya yi imani cutar ta samo asali ne daga dabbobi amma ba a tantance ina ta shiga kafin ta yadu ga dan Adam ba.
A birnin Wuhan ne aka fara gano cutar, kuma Liang ya ce babu hujjar cewa ta yadu a birnin kafin gano wadanda suka fara kamuwa da ita a hukumance a watan Disamban 2019.
Ya ce mai yiwuwa kwayar cutar ta fara bazuwa a wasu yankunan duniya kafin a gano ta a China.