Minista a Ma’aikatar Lantarki, Goddy Jedy-Agba, ya ce har yanzu alwashin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha na cire ’yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci yana nan daram.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a rana ta biyu ta taro kan makamashi a Najeriya na 2022, wanda ya gudana da intanet.
- Ya kashe abokinsa da kahon dabba saboda ya ki saya masa giya
- NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilin Ci Gaban Wahalar Mai —Masani
Goddy ya ce za a sami nasarar ce a karkashin shirin gwamnatin kan makamashi na ETP.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dai ya kaddamar da shirinsa na ceto ’yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci kafin nan da shekarar 2030.
Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Lantarkin, Kachollum Daju, ce ta bayyana hakan yayin da take jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi.
A cewar Ministan, shirin na ETP zai ceto ’yan Najeriyar da ba za su gaza miliyan 100 ba.
“Shirin zai kuma kirkiro da hanyoyin samar da makamashi na zamani ga dukkan ’yan Najeriya, sannan ya magance matsalar rasa ayyukan yin da ake yi a fannin man fetur sakamakon sabbin dabarun na zamani,” inji Ministan.
Sai dai tabbacin na zuwa ne ’yan kwanaki bayan Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar da wasu sabbin alkaluman da suka nuna cewa akalla ’yan Najeriya miliyan 133 suka sake fadawa kangin talauci.