Biyu daga cikin ’yan matan Chibok din da aka kubutar daga hannun Boko Haram sun ce har yanzu akwai takwarorinsu 20 a dajin Sambisa, shekara takwas bayan sace su.
Mary Dauda da Hauwa Joseph, biyu daga cikin daliban Sakandiren Gwamnati da ke Chibok da aka sace a shekarar 2014, sun bayyana haka ne bayan sojojin rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai sun kwato su daga ’yan ta’addan.
- Zan bar Najeriya fiye da yadda na same ta – Buhari
- Sojoji sun mika ’yan matan Chibok 2 ga gwamnatin Borno
Sun bayyana hakan ne lokacin da suke zantawa da manema labarai ranar Talata a barikin sojoji na Maimalari da ke Maiduguri.
Mary Dauda wacce ta bayyana irin halin da ta tsinci kanta, ta ce an aurar da ita ga ’yan ta’adda, bayan an sace ta tana da shekara 18.
Ta ce sai da ta shafe tsawon kwanaki tana tafiya a cikin dajin mai matukar hatsari kafin ta sami agaji.
Ta ce da kyar ta samu ta gudo daga dajin bayan ta yi karyar cewa tana so ta je ta ga wata ’yar uwarta a garin Ngoshe, inda a kan hanya ta hadu da sojoji.
A nata bangaren, Hauwa Joseph ta ce an aurar da ita ta karfin tsiya ga Amir Abbah, wani Kwamandan Boko Haram, wanda daga bisani sojoji suka kashe shi.
Ta ce a kashin kanta ta tsere daga sansanin bayan sojojin sun kai wani mummunan hari ranar 12 ga watan Yunin 2022.
A nasa bangaren, Kwamandan Rundunar ta Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa, ya ce matan biyu na cikin ’yan matan Chibok din da aka sace.
A ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne Boko Haram ta sace ’yan mata kusan 276 daga makarantar, galibinsu ’yan tsakanin shekara 16 zuwa 18.
Sai dai duk da ceto da yawa daga cikinsu, har yanzu akwai ragowar ’yan matan sama da 100 da ba a san inda suke ba. (NAN)