✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu akwai burin da nake so in cim ma a Super Eagles – Enyeama

Gola kuma Mataimakin Kyaftin din kungiyar Super Eagles na Najeriya bincent Enyeama, ya ce har yanzu akwai burin da yake so ya cim ma a…

Gola kuma Mataimakin Kyaftin din kungiyar Super Eagles na Najeriya bincent Enyeama, ya ce har yanzu akwai burin da yake so ya cim ma a Super Eagles.
Enyeama mai kimanin shekara 31 wanda Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta zaba a matsayin Gwarzon Gola na Afirka, ya bayyana hakan ne, sakamakon jita-jitar da ake yadawa cewa ya yi ritayar buga wa Najeriya wasa.
Ya karyata jita-jitar ne a lokacin da ya yi wata hira da shafin intanet na gidan Talabijin din Super Sport a ranar Lahadi.
 “Ban ce na daina buga wa Najeriya wasa ba, na ce zan y i shawara da iyalina da kuma abokaina. Amma har yanzu akwai burin da nake so na cim ma a Super Eagles.”