Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin ya ce har tukin tasi ya taba yi lokacin da tsohuwar Tarayyar Soviet ta rushe a shekarar 1991 don ya tsira da mutuncinsa.
A wani sabon fim da aka fitar a kwanan nan kan tarihin kasar, Shugaba Putin ya bayyana rushewar tsohuwar tarayyar a matsayin babbar barazana ga tarihin kasar, inda ya ce ya tilasta wa ’yan kasar da dama neman wasu hanyoyin samun kudi.
- ’Yan gudun hijirar Afghanistan 6 sun mutu a hatsarin mota a Iran
- An harbe matafiya 2, an sace wasu da dama tsakanin Kaduna da Zariya
Ya ce, “Wani lokacin sai da na nemi karin hanyoyin samun kudi a matsayin direban tasi. Abu ne da ba zan iya bayyana wa ba.”
A farkon shekarun 1990, Putin ya taba aiki a ofishin Magajin Garin St. Petersburg, Anatoly Sobchak.
Ya ce daga bisani ya ajiye mukaminsa a shekarar 1991 bayan an yi wa Shugaba Mikhail Gorbachev juyin mulki, lamarin da ya kai ga wargajewar kasar.
Tsokacin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ta jibge jami’an tsaro sama da 90,000 a kan iyakarta da Ukraine, lamarin da ya kara jefa barazanar cewa tana yunkurin mamayeta ne.
Sai dai Rashan ta musanta labarin, inda ta ce Ukaraine din kawai na neman gindin zama ne a wajen kungiyar Kawance ta NATO.