✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har Maroko muke zuwa safarar tumatir – ’Yan Kasuwa

Shugaban Kasuwar Sasa Ibadan, Alhaji Alasan JK ya shaida wa Aminiya cewa a yanzu kasashen ketare suke zuwa domin yin safarar tumatir a sakamakon ƙarancinsa…

Shugaban Kasuwar Sasa Ibadan, Alhaji Alasan JK ya shaida wa Aminiya cewa a yanzu kasashen ketare suke zuwa domin yin safarar tumatir a sakamakon ƙarancinsa a Najeria.
Ya ce suna zuwa ƙasashen da suka haɗa da Morokko da kamaru ko  Nijar, Kwatano, Togo ko Ghana domin  sayen tumatur sakamakon annobar tsutsa da ta cinye tumatur din gida Najeriya. Hakan ya sa magidanta amfani da tumatur din leda ko na gwangwani. “Shi dai wannan tumatur na kasar Morokko, ana shigo da shi ne cikin ɗan akwati, inda ake sayar da shi kan farashin Naira dubu 12.” Inji shi.
A sakamakon illar da tsutsar nan da ake yi wa laƙabi da ‘Ibolar Tumatur’ ta yi wa mafi akasarin tumatur ɗin da ake nomawa a jihohin Arewacin ƙasar nan, abin da ya janyo ƙarancinsa a kasuwannin Najeriya da ma uwa-uba haddasa tsadarsa ta yadda ya gagari aljihun mai ƙaramin ƙarfi, a inda ake sayar da kwandon timatir a kan Naira dubu 30 zuwa 35 a kasuwannin jihohin Legas, Oyo, Ogun da sauransu.
Shugaban kasuwar ya jinjina wa Gwamnatin Tarayya da gwamnonin Arewa bisa kokarinsu na magance matsalar tsutsar wadda ta janyo wa ɗinbin manoma asara. Ya ce Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru el-Rufa’i ya ƙoƙarta wajan shawo kan matsalar. Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ɗauki ƙwararan mataken da za su magance irin haka a nan gaba.