Na fara wannan rubutu ne zuciyata cike da takaici, kunci da bacin rai.
Na tsinci kaina a cikin wannan yanayinnne sakamakon ta’addancin da ya faru cikin makon da ya gabata na kisan gillar da wasu matasan Kirista suka yi wa wasu matafiya su kimanin 30 a kan wata babbar hanya da ke cikin garin Jos na Jihar Filato.
Matafiyan sun gamu da ajalinsu a dalilin taka sawun barawo da suka yi, yayin da suke kokarin kauce wa cunkoson ababen hawa a cikin gari.
Sai suka yi kuskuren bin wata hanyar bayan gari don yin ratse su wuce zuwa Abuja daga nan kuma su dauki hanyar komawa Jihar Ondo a Kudu Maso Yammacin Najeriya, inda ’yan uwa da iyalansu suke.
Rahotanni sun bayyana cewa, wadannan mutane wadanda akasarinsu Fulani ne, mabiya darikar Tijjaniyya, sun fito ne daga Jihar Bauchi, inda aka gudanar da babban taron zikiri na kasa da addu’o’in zaman lafiya a gidan Babban Shaihun Darikar nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, albarkacin shiga Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1443 Bayan Hijira da aka yi. Amma hanya ta bi da su ta Jos, babban birnin Jihar Filato a kan hanyarsu ta komawa gida.
Sai dai sakamakon kaddara da aka ce ta riga fata, ko kuma tsautsayi da ake cewa ba ya wuce lokacinsa, wadannan matafiya suka shiga garin na Jos a lokacin da al’ummar Irigwe ke cikin makokin kashe-kashen da suke zargin maharan Fulani sun kai kan mutanensu a kauyukan Miango a Karamar Hukumar Bassa, yankin da ke makwabtaka da babban birnin jihar, a dalilin rikita-rikitar da ta dade tana aukuwa tsakanin manoma da makiyaya a yankin, kuma take ci gaba da haifar da asarar rayuka da dukiyoyi, daga kowanne bangare.
An rawaito Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Filato na bayyana cewa, fusatattun matasan kabilar Irigwe ne suka far wa wadannan matafiya Fulani da ke cikin manyan motoci kirar homa bas guda biyar, yayin da su kuma mutanen Irigwe suka dauko gawarwakin ’yan uwansu da aka kashe za su je wajen binnewa.
Ganin motoci cike da bakin fuska masu kamannin Fulani a cikin jerin motocin da ke hanya suna jiran masu wucewa da gawa wadanda ke sanye da bakaken kaya su wuce, ya sa su kara harzuka, inda suka far musu da jifa da duwatsu da sauran makamai da aka rika fitowa da su daga bisani, don hallaka wadannan matafiya da suke yi wa kallon makiya, wadanda kuma suke zargin ’yan uwansu ne suke kashe musu nasu ’yan uwan su ma.
Sakamakon abubuwan da suka faru dai na keta da mugunta, rahotanni sun ce an kashe mutanen da ba su gaza 30 ba, duk da yake a hukumance rahoton hukumar ’yan sanda na farko ya bayyana cewa mutum 22 ne aka kashe yayin da ake ci gaba da neman wasu da suka fantsama cikin duwatsu, da gidajen jama’a, don neman mafaka.
– Farautar matafiya a Filato
Kwana goma kafin wannan bakar rana ta Asabar, nesa kadan da inda wannan ta’addancin ya auku a yankin Gada-Biyu, wasu matasa sun far wa wasu matafiya Fulani da suka je wucewa da shanu a wasu motoci biyu za su kai Abbatuwa, don sayarwa ga masu fawa.
Nan ma haka aka kashe wasu da kona motocin.
Abin da ya kara sanya fargaba da taraddadi a zukatan matafiya musamman mazauna garin Jos, wadanda sanin halin da hanyar ke ciki ya sa suke kaurace wa bin ta. Sai dai baki da suke shigowa cikin rashin sani.
Jihar Filato ta dade da kasancewa tarkon mutuwa, musamman ga matafiya wadanda sau tari suke shiga garin Jos ta makwabtan kauyuka inda ake yawan samun tashe-tashen hankula, sakamakon rikicin kabilanci da na addini da ya dabaibaye jihar.
Rayuka da dama sun salwanta a irin wannan fadawa cikin tsautsayi da kaddara da matafiya baki kan yi, a hannun matasan kabilun Filato, wadanda a duk lokacin da suka samu wata damuwa da abokan zamansu makiyaya ko mazauna jihar, sai su fita su datse kan manyan hanyoyin da suka ratsa ta jihar suna farautar duk wani da suka ga yana kama da wata kabila da suke rikici da ita, musamman ma dai Hausawa ko Fulani.
Ba za mu manta da kisan gillar da aka yi wa Marigayi Janar Alkali ba, a kan hanyarsa ta zuwa Jihar Bauchi, inda ya biyo ta hanyar Jos.
– Abin ya zama ruwan dare
Wannan halayya ta tare hanya a rika afka wa matafiya da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, ya kusan zama ruwan dare a kasar nan, musamman ma dai a yankin Arewa.
Ya sha faruwa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda mazauna kauyukan da ke kan hanya sukan fita su datse hanya su rika kisa da lalata ababen hawa da ke wucewa ta kan titin gwamnati, saboda kawai suna tarzoma ko nuna rashin jin dadi ga wani abu da ya ke faruwa da al’ummarsu.
Ba a hanyar Abuja ba, hatta a yankin Kudancin Jihar Kaduna ma inda ake samun fadace-fadace tsakanin manoma da makiyaya a yankin, wannan salon suke amfani da shi, wajen datse hanya suna binciken ababen hawa ko za su samu wani matafiyi da ya yi kama da kirar abokan gabarsu, don kawai su huce fushinsu su dauki fansar abin da suke zargin an yi musu.
A daidai lokacin da nake wannan rubutu ma, akwai wasu rahotanni da ba su inganta ba da ke gargadin matafiya su kauce wa bin hanyar Kagoro a yankin Kudancin Kaduna, saboda yadda wasu bata-gari ke tare hanya suna cutar da matafiya.
Rikicin kabilanci a Jihar Gombe ya sha haifar da irin haka, a wayi gari wani sabani tsakanin mazauna jihar ya sa wasu marasa tunani su hau kan hanya suna buge masu ababen hawa da ba su ji ba, ba su gani ba.
– Rashin tsaro da lalacewar hanyoyin
Ba ma batun rikicin kabilanci ba, dama wasu hanyoyin da dama sun gagara biyuwa ga matafiya saboda rashin tsaro, sace-sacen ’yan bindiga masu garkuwa da mutane, da ’yan ta’adda a yankin Arewa Maso Gabas da suka sa ala tilas wasu manyan hanyoyin suka daina biyuwa ta dadin rai ga matafiya.
Ga kuma wata matsalar da ita ma har yanzu aka kasa magance ta, wato matsalar lalacewar manyan hanyoyi da ke zama mutuwa kusa ga matafiya, inda rayukan ’yan Najeriya da dukiyoyinsu ke salwanta, saboda rashin kyan hanya.
Dubi dai misalin hanyar Zariya zuwa Saminaka zuwa Jos, hanyar da ta kusa mutuwa baki daya.
Direbobi da dama sun kaurace mata, sun gwammaci su yi zagaye, wanda ke jefa su cikin wani hadarin.
– Gwamnati ko ’yan kasa?
Muna kira ga hukumomin da abin ya shafa su kara zage damtse wajen ganin sun gyara manyan hanyoyin kasar nan da samar da ingantaccen tsaro da zai cire fargaba da tsoro a zukatan direbobi da sauran matafiya.
A lokaci guda kuma muna kira ga ’yan Najeriya musamman mazauna garuruwan da ke bakin hanya su guji amfani da wadannan hanyoyin a matsayin wani makami na cimma burinsu na ramuwar gayya, ko huce haushi kan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.
Tabbas wannan kuskure ne babba, kuma bam ne da zai iya jefa kasar nan cikin mummunar matsalar tsaro.
Domin idan har aka kyale irin abin da ya faru a Jos ya ci gaba da faruwa ba a dauki tsattsauran mataki ba a kai, to lokaci zai zo da al’ummar wata jiha da aka taba mutanensu za su ce su ma ba su yarda ba, su shiga tare wasu matafiya a nasu bangaren suna daukar fansa.
Hakan ba zai haifar wa kasar nan da kyakkyawan sakamako ba!
An jiyo cikin wata sanarwa da kakakin Fadar Gwamnatin Jihar Ondo, Richard Olatunde ya fitar yana mai isar da sakon Gwamnan Jihar Rotimi Akeredolu cewa, jama’ar jihar su kwantar da hankalinsu bisa abubuwan da suka faru na kisan gillar da aka yi wa wasu ’yan jihar a Jos, sakamakon jajantawar da Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya yi masa kan abin da ya faru.
Idan lamarin yana kaiwa ga haka, har ta kai gwamnati da gwamnati na musayar maganganu kan rashin hankalin da wasu suka nuna a kan matafiya, to lallai alamu na nuni da wata rana abin da zai biyo baya ba zai yi wa kowa dadi ba.
Ya kamata ’yan Najeriya a duk inda suke su kasance masu tausayawa juna da hadin kai, domin a samu ingantaccen tsaro da zaman lafiya.
Mu zama masu aiki da hankali, mu daina biye wa son zuciyoyinmu.
Allah Ya jikan rayukan da aka rasa. Amin
Abba Abubakar Yakubu, ya rubuto wannan sharhi ne daga Jos, Jihar Filato.