Ido wani sashe ne na jikin dan Adam mai matukar amfani, wanda da shi ne mutum ke amfani wajen gani da kuma tura wa kwakwalwa sakon abin da ya gani.
Muhimmancinsa ne ya sa masana kiwon lafiya suka bayyana wasu hanyoyi biyar da za a bi wajen inganta shi kamar haka:
- Kwamitin yakin zaben Buhari ya koka da Gwamnatin APC
- Muna bukatar sojoji su kare layukan dogo a Najeriya — Amaechi
1. Motsa jiki:
Motsa jiki na da matukar muhimmanci da tasiri ga lafiyar jiki, ciki har da ido.
Ido na da nashi irin atisaye da ake masa, mutum zai juya ganinsa zuwa bangaren dama sai ya kwanta da barin jikinsa na hagu na tsawon minti uku.
Sannan sai ya sake juya ganinsa zuwa bangaren hagu ya kwanta da bangaren jikinsa na dama, shi ma na tsawon minti uku.
2. Abinci mai gina jiki:
Cin lafiyayyen abinci mai gina jiki yana taimaka wa lafiyar ido sosai; musamman cin abinci mai dauke da ganyayyaki na da matukar tasiri ga lafiyar ido.
3. Dokar 20-20-20:
Ga wanda yake yawan amfani da kwamfuta, yana da kyau ya bi dokar 20-20-20.
Doka ce ta bukaci idan ana amfani da kwamfuta, to ya kamata duk bayan minti 20 a kalli wani abu wanda ya kai tazarar kafa 20 har na tsawon dakika 20.
4. Taba-Sigari:
Ga wanda yake shan sigari yana da kyau ya daina domin sigari na haddasa cututtuka kamar cutar daji, ciwon huhu, rage karfin gani da sauransu.
5. Tarihin lafiyar idanu: Yana da kyau mutum ya ziyarci likita don sanin tarihin lafiyar idanun danginsa, ma’ana idan akwai tarihin matsalar gani hakan zai taimaka wajen shawo kanta kafin ta zama babba.