Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya bayyana aniyarsa ta gadar kujerar Shugabancin Kasar nan, da zarar shugaba Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa a 2023.
Ya bayyana haka ne a wata tattaunawarsa ta musamman ranar Litinin da gidan talabijin na Arise.
- Juyin mulki: Sojojin Sudan sun hallaka masu zanga-zanga 2, sun raunata 80
- Sojojin Najeriya sun kera manyan jiragen yakin ruwa guda 4
A cewarsa, yana da dukkanin wata nagarta da ake nema a wajen Shugaban Kasa.
“Da yardar Allah ba zan samu sukuni ba har sai an rantsar da ni a ranar 29 ga watan Mayun 2023, a matsayin magajin Shugaba Buhari,” inji shi.
Kazalika, ya yi karin haske kan yanayin da samu Jihar Kogi bayan zama gwamna a 2016.
Ya ce, “Na gaji jihar nan lokacin da take tsaka da miyagun ayyuka
“Don haka na yi aiki tukuru wajen gina tare da shigar da matasa da mata cikin gwamnatina.
“Amma yanzu Kogi ta samu ci gaba mai tarin yawan gaske, wanda na daga cikin irin ci gaba da kasa ke so ta samu,” cewar Yahaya Bello.