✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Hana shigo da kaji ya bude mana kasuwa ne’

A lokacin da ’yawa-yawan  ’yan kasuwa ke korafin fuskantar koma-bayan ciniki a kasuwancinsu. Masu sana’ar sayar da kaji yabawa suka yi da bunkasar ciniki da…

g Shugaban Masu Sayar da Albasa a Kasuwar Nyanya Malam Magaji A BabaA lokacin da ’yawa-yawan  ’yan kasuwa ke korafin fuskantar koma-bayan ciniki a kasuwancinsu. Masu sana’ar sayar da kaji yabawa suka yi da bunkasar ciniki da suka ce suna samu a wannan lokaci.
Jagoran masu sayar da kaji na kasuwar Nyanya da ke Abuja Malam Aliyu Ya’u ne ya bayyana hakan a yayin wata zantawa da Aminiya.
Ya ce hana shigo da daskararrun kaji daga kasashen ketare da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi, ya sa jama’a sun koma sayan kajin gidan gona da manoman kasar nan ke kiwo da kuma kajin gida da suke sayarwa, hakan inji shi ya sa suna samun ciniki.
Hakazalika, ya ce gabanin zuwan wannan gwamnatin, jama’arsu na asaran tarin kaji da kuma kudi a kan hanyarsu ta dawowa daga jihohin arewa, inda suke sayo kajin a sakamakon bata lokaci da suke yi a shingayen jami’an tsaro. “Haka muka yi ta fama a lokacin, bayan mun bi dogon layin mota a shingayen tsaro a karshe sai su ce mu yi fakin na mota, a nan muke rasa kaji musamman  ma na gidan gona wadanda ba sa jure wuya sannan kuma a karshe sai su bukaci kudi daga hanunmu,” inji shi.
Malam Aliyu Ya’u ya ce a yanzu suna shiga duk wani kauye da ke da wadatar kaji don sayowa sabanin a baya da matsalar tashe-tashen hankula na kabilanci ko na addini suke hanasu zuwa, inda ya yi misali da Jihar Filato.
A nasu bangaren ’yan kasuwa da ke sayar da kayan abinci kokawa su ka yi da isgili da suke fuskanta daga abokan huldarsu. Shugaban masu sayarda albasa a kasuwar ta Nyanya Abuja, malam Magaji A. Baba wanda ya yaba da nasarar da gwamnatin Shugaba Buhari ta samu a bangaren samar da tsaro da kuma yaki da cin hanci, ya ce tsadar da kayan abinci suka yi a sakamakon hana shigo da shinkafa daga iyakokin da ba na ruwa ba, ya sa jama’a na komawa wasu nau’ukan abinci da ba sai an sa masu albasa ba a wajen hadasu.
Ya ce “duk da kasancewar albasa da muke sayarwa a gida Najeriya a ke  nomata sannan farashinta bai kara ba, masu sayarta na sayan kadan ne kasa da adadin da su ka saba saya. Sannan da magana ta hadamu sai su ce canji ne ya jawo hakan ba tare da la’akari da tarin alheri da canjin ya kawo ba. Ba a kasuwa ba kadai muke fuskantar wannan isgili ba, ko a mota mu ka shiga idan wata magana ta hadamu sai su ce ai canji ne ba mu muka zabi canji ba.”
Daga nan ya yi kira ga Shugaban kasa Buhari da ya yi wani abu a kan matsalar tsadar kayan abinci da kuma ta karancin kudi a hannun jama’a.