✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hana matan Afghanistan zuwa jami’a: Saudiyya da Turkiyya sun yi Allah-wadai da Taliban

Kasashen sun ce sam dokar ba Musulunci ba ce

Kasashen Turkiyya da Saudiyya sun yi Allah-wadai da kakkausar murya da matakin da gwamnatin Taliban a Afghanistan ta dauka na haramta wa matan kasar zuwa jami’o’i.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu, ya fada a ranar Alhamis cewa sam haramcin ba Musulunci ba ne kuma babu tausayi a cikin shi.

Da yake jawabi ga wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Yemen, Mevlut ya bukaci Taliban da ta soke dokar.

“Wacce illa ce a ciki idan mata sun yi ilimi? Wacce illa hakan zai yi wa Afghanistan? Akwai wata madogara a addinin musulunci kan daukar wannan matakin? A zahirin gaskiya ma Musulunci ya goyi bayan ilimin ’ya’ya mata ne bai hana su ba,” inji Ministan.

Ita ma Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta bayyana takaicinta da matakin, kamar yadda ta bayyana haka a matsayin abin mamaki ga duk kasashen Musulmai, a cikin wata sanarwa ranar Laraba.

Turkiyya da Saudiyya dai sun zama na baya-bayan nan daga jerin kasashen Musulman da suka yi kakkausan martanin bayan na kasar Qatar, wacce ita ce ta kasance mai shiga tsakanin Taliban da Amurka.

Ko a ranar Alhamis sai da wasu mata a kasar suka shirya zanga-zangar nuna kin jinin sabuwar dokar a wasu titunan Kabul, babban birnin kasar, suna rera wakokin neman ’yanci.

Kazalika, tuni Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomin kasa da kasa da ma kasashe da dama ne suka bi sahu wajen yin Allah-wadai da matakin na Taliban.

Dokar dai na cikin jerin dokokin da gwamnatin ta sanya wa mata tun bayan da ta karbi mulkin kasar a watan Agustan 2021.

A baya dai gwamnatin ta sanar da hana mata zuwa aikin gwamnati sannan ta ce hatta fita daga gida dole sai da muharraminsu za su yi ta.