Ahmadu Haruna matashi ne dan kimanin shekara 30 da ke zaune a Tudun Wada Kaduna wanda ya rungumi sana’ar faci a matsayin hanyar samun abincinsa. Ya yi shekaru da dama a wannan sana’a sai dai tun bayan da gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa dokar hana masu babura yin acaba a watan Mayun da ya gabata matashin ya ce harkar sana’ar ta tabarbare a hirar da suka yi da wakilinmu kamar haka.
Aminiya: Mene ne cikakken sunanka? Sunana Ahmadu Haruna
Aminiya: Shekararka nawa?: Na kai kimanin shekara 30.
Aminiya: Batun karatu fa? Na yi firamare daga nan na shiga sakandare amma ban karasa ba na tsaya don a wancan lokaci mahaifina Allah Ya yi masa rasuwa. Saboda haka ne na rungumi sana’ar hannu.
Aminiya: Mece ce sana’ar da ka dogara da ita a halin yanzu? Ina yin sana’ar faci ne.
Aminiya: Kafin wannan sana’a ka taba yin wata? Eh, na taba yin sana’ar gyaran babur (bespa) sannan na koyi gyaran na’urar janareto kuma na sayar da rake inda daga baya na koyi wannan sana’a ta faci, kuma alal hakika ta karbe ni don a halin yanzu da ita nake ci, nake sha har nake taimakon wasu.
Aminiya: A wace shekara ka koyi wannan sana’a ta faci? Na koya ne tun a shekarar 2009 watau kimanin shekaru biyar da suka gabata. Kuma a wajen wani maigidana da ake kira Ahmed Mohammed da ke zaune a kusa da gidan mai na Bushara, a can na koya. Kafin ya yaye ni sai da na shekara bakwai ina koyon wannan sana’a a wajensa.
Aminiya: To kai kuma mutane nawa ka yaye daga lokacin zuwa yanzu? A gaskiya na yaye akalla mutum biyar da yanzu haka suke cin gashin kansu.
Aminiya: Yaya batun hana acaba da gwmanatin Jihar Kaduna ta yi a kwanakin baya, abin ya shafe ka? A gaskiya zan ce na fi kowa jin jiki. Don a da kafin a hana yin acaba a Jihar Kaduna a kullum nakan yi cinikin da bai gaza Naira dubu 3 zuwa dubu 5 ba, don nakan yi wa akalla mashina 30 zuwa 50 faci a kullum baya ga motoci da masu tura baro da sauransu amma daga lokacin da aka hana zuwa yanzu da kyar nake yin facin Naira dubu 1 ko babura biyar a rana.
Aminiya: To sai na ga kamar akwai masu Keke-Napep su ba sa kawo muku faci ne? Eh akwai bambancin Keke-Napep da babura ko mashina. Su mashin ko babur sun fi saurin yin faci a duk lokacin da suke kan aiki fiye da Keke-Napep. In ka lura Keke-Napep tana amfani ne da kafa uku kuma akasarinsu sababbi ne, tayoyinsu ba su fara yin faci ba kuma ko da sun yi facin ma suna da safaya taya (spear tire) da za su lika su cigaba da sana’a ba tare da matsala ba. Amma shi mashin ko babur dole idan ya yi faci ya tsaya ya nemi mai faci idan ba haka ba aiki ba zai yiwu ba. Kuma wani dalili shi ne ba su yi yawan da ya kai na babura ko mashina ba.
Aminiya: Wadanne nasarori ka samu a harkar faci? Na samu nasarori da dama, kadan daga ciki su ne na auri mata biyu na sayi mota, ina taimakon ’yan uwana sannan ina biyan bukata ta ba tare da na nemi taimakon wani ko wasu ba. Haka kuma na koyawa wasu da dama hanyar samun dogaro da kai.
Aminiya: Wadanne matsaloli kuma kake fuskanta? Babbar matsalar ita ce na rashin isasshen jari don bunkasa wannan sana’a tawa.
Aminiya: Mene ne burinka? Babban burina shi ne in samu jarin da zan fadada wannan sana’a a sassa daban-daban na jihar nan da ma kasa baki daya.
Aminiya: Jarin nawa mutum ke bukata idan yana son ya fara sana’ar faci? Akalla duk mai son fara wannan sana’a sai ya tanadi Naira dubu 40 zuwa 50 don sayen kayyakin yin faci. Sannan idan mutum yana bukatar ya bude babban shagon yin faci ne zai bukaci akalla Naira dubu 100 zuwa dubu 120.
Aminiya: Ka taba samun tallafi daga wajen wani ko hukuma? Gaskiya ban taba samun tallafin kudi ko na kayan iaki daga wajen wani ko hukuma ba. Duk abin da ka gani a nan ni na saye su da kudina.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga matasa masu zaman kashe wando? Ina kiran su tashi tsaye su nemi na kansu musamman a bangaren sana’ar hannu. Zaman banza ba nasu ne ba kuma ba shi da wani tasiri.
Aminiya: Ita kuma gwamnati wane kira kake da shi zuwa gareta? Ta rika tallafa mana da jari ko kayayyakin aiki hakan shi zai sa matasa da dama su rungumi sana’ar hannu.
Aminiya: Harkar iyali fa? Ina da mata biyu da ’ya’ya biyu.