✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hamshakan masu kudin duniya sun tafka asarar tiriliyan N518 a 2022

Rahoton ya binciko yadda hamshakan masu kudin duniya suka tafka asara.

Wani rahoto da jaridar nan mai bin diddigin dukiyar masu kudi a duniya, Bloomberg, ta fitar ya ce akasarin mutanen da suka fi arziki a duniya sun samu koma bayan da ba za a mantawa ba a shekara ta 2022.

Rahoton an Bloomberg mai taken kididdigar biloniyoyi ya ce, dukiyar mutanen da suka fi kudi a duniya kusan Naira tiriliyan 518 wato Dala tirliyan daya da biliyan 400 ne suka salwanta.

A cewar rahoton masu kudin da yawansu ya kai 500, sun tafka asara ne a bangaren kudi da wasu kadarorinsu.

Ya ce babban abin ciwon kamar yadda abubuwan suka bayyana, duniya ce da kanta ta janyo babbar asarar.

Abubuwan da rahoton ya dora wa alhakin wannan asarar ta dukiya mai yawa, sun hada da zargin damfarar makudan kudin kirifto da mai rusasshen Kamfanin FTX, Mista Sam Bankman-Fried ya yi.

Haka zalika, yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine ya janyo takunkuman da suka durkusar da harkokin kasuwanci musamman a tsakanin mashahuran masu kudin kasar.

Haka kuma irin halin da Mista Elon Musk sabon mai Kamfanin Twitter wanda dukiyarsa yanzu ba ta fi Naira tiriliyan 56 da biliyan 25 (Dala biliyan 138), wato kasa da abin da ya mallaka a farkon shekarar 2022.

Mista Elon Musk ya kafa tarihin zama mutum na farko da ya tafka babbar asarar dukiya ta Naira tiriliyan 83 (Dala biliyan 200) a cikin shekara daya, inda a farkon bara, mai Kamfanin na Tesla ke da jimillar dukiya ta Naira tiriliyan 132 da biliyan 800 wato (Dala biliyan 320).

A halin yanzu yana da jimillar dukiya ta Naira tiriliyan 56, sannan ya rasa matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a duniya.

Elon Musk ya zama mutum tilo da ya fara da tara dukiya mai dimbin yawa, ya kuma tafka asara da ba a taba gani ba a tarihin dan Adam.

Da farko ya karbi ragamar Twitter Ya fara kasuwancin Twitter cikin rawar kai inda nan take ya kori sama da ma’aikata 7,000 wanda hakan ya yi sanadiyar dakatar da tallace-tallace a kafar sada zumuntar.

Twitter ta fuskanci matsanantanciyar asara tun daga lokacin da Musk ya karbi ragamar tafiyar da kamfanin.

Hakazalika ya kuma kirkiro da tsarin biyan kudade ga dukkan masu amfani da shafukan kafar wanda mutane da dama suka bari.

Baya ga haka, rahoton na Bloomberg ya ce idan aka duba yadda hauhawar farashi da kuma irin tsauraran matakan da manyan bankunan kasashe suka dauka a shekarar 2022 za a iya cewa ta kasance wata bakar kaddara ga biloniyoyin duniya, wadanda dukiyar ta yi matukar karuwa a lokacin annobar COVID-19.

Ga mafi yawan masu kudi, gwargwadon yawan kudin da suka samu a shekarar annobar cutar kwarona, gwargwadon girman asarar da suka tafka kenan.

Jaridar Bloomberg ta ce Mista Elon Musk da Mista Jeff Bezos da Mista Changpeng Zhao da Mista Zuckerberg su kadai sun yi asarar Naira tiriliyon 162 da biliyan 680 (Dala biliyan 392) a cikin tsagwaron dukiyarsu.

Sai dai wani abin karfafa gwiwa shi ne, ba duka aka taru aka zama daya ba, ga wannan rukuni na masu kudin duniya, inda wani rukunin suka samu babban ci gaba a dukiyar tasu.

Hamshakin mai kudin nan dan kasar Indiya Mista Gautam Adani ya samu karin tagomashi, bayan da ya zarce Bill Gates da Warren Buffet a jerin masu kudin duniya.

Hakazalika, su ma wasu dangin masu kudin duniya kamar Kochs da Mars clan, duk sun samu kari ne a cikin dukiyar tasu.