Isra’ila ta kai hari a Zirin Gaza inda jiragen yakinta suka lalata wasu wurare da take zargin masana’antun makaman kungiyar Falasdinawa ta Hamas da ke iko da yankin ne.
Ministan Lafiya na gwamnatin Hamas ta Falasdinu ya tabbatar da harin, sai dai ya ce babu ko mutum guda da ya rasa ransa ko ya ji rauni sakamakon harin yadda.
- Sojoji sun kashe Kwamandan ISWAP Ammar Bin-Umar
- Ba za mu yaki ’yan bindiga da jiragen Super Tucano ba sai 2023 —Gwamnati
Rundunar Ezzedine al-Kassam, reshen aikin soji na kungiyar Hamas ta ce, “Mayakanmu sun mayar da martani da makamai masu linzami da misalin karfe 10:35 agogon GMT a safiyar Talata.”
Harin na zuwa ne bayan Isra’ila ta kakkabo wani roka da aka harba daga Zirin Gaza zuwa Kudancin kasar a ranar Litinin, a karon farko cikin watanni da ake dambarwa game da Masallacin Kudus da ke gabashin birnin.
Kawo yanzu dai ba a samu asarar rai ko ta dukiya ba, sannan babu wata kungiyar Falasdinawa da ta dauki alhakin kai harin, wanda Isra’ila ta ce ta ne suka harbo makamin.
Kungiyar Hamas ta yi gargadin cewa muddin Isra’ila ta kawo yamu a Masallacin Kudus to takala ce, bayan dakarun Isra’ila sun yawaita kai samame a masallacin a ’yan kawanakin nan tare da kame daruruwan Falasdinawa da kuma jikkata wasu da dama.
Falasdinawa na zargin Isra’ila da kutse cikin Masallacin Kudus a cikin watan Ramadana mai alfarma.
Ita kuma tanar zargin Falasdinawa masu zanga-zanga da neman hana Musulmi yin ibabadusnu da kuma hana ziyarar da Yahudawa a yayin da suke kammala azuminsu.