Hamas za ta yi nasara a kan ƙasar Isra’ila komai daren daɗewa, a cewar tsohon shugaban ƙungiyar, Khalid Masha’al.
Ya bayyana cewa haka ne a jawabinsa a safiyar Litinin da ake cika shekara guda da fara rikicin Isra’ila da Hamas wanda aka faro ranar 7ga Oktoba, 2023, bayan ƙungiyar ta kai wa Isra’ila hari mafi muni a tarihi.
Khalid Masha’al ya miƙa godiya ga gwamnatin ƙasar Iran da ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Lebanon da kuma Houthi da ke Yaman bisa taimakon da suke ba wa ƙungiyar Hamas.
Sannan ya buƙaci ƙasashen Labarawa da su taimaka wa al’ummar Falasɗinawa da tallafin kuɗaɗe a Zirin Gaza.
- Iran ta karrama kwamandan da ya kai wa Isra’ila hari
- Yaƙin Gaza: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 41,000 ta sa 2.5m gudun hijira a shekara guda
Khalid Masha’al ya jaddada cewa Kodayake nasarar Hamas a kan Isra’ila tana iya zuwa da jinkiri, amma yana da yaƙinin cewa babu makawa sai ta tabbata.
Ya ƙara da cewa harin 7 ga Oktoba da Hamas ta kai wa Isra’ila gagarumar nasara ce ga ƙungiyar Hamas kuma ta cimma hadafinta.
Ya bayyana cewa ɗaukar matakin harin wanda shi ne mafi muni a tarihin Isra’ila ya zama dole ne, saboda an rufe ƙofofin tattaunawar siyasa.
A cewarsa, ganin Isra’ila ta kasa cimma manufarta a Zirin Gaza ne ta ƙaddamar da yaƙi a Gabashin ƙasar Lebanon.
Ya kuma yi zargin cewa a halin yanzu Isra’ila tana shirya maƙarƙashiya ga ƙasashen Jordan da Masar.