✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin taskun da Musulmin Rohingya ke ciki a Bangladesh

Musulmi ’yan kabilar Rohingya da ke gudun hijira a Bangladesh na tunanin komawa gida, inda sojojin Myanmar ke musu kisan kiyashi

Musulmi ’yan kabilar Rohingya da suka yi gudun hijira zuwa Bangladesh sakamakon kisan kiyashi da sojojin kasar Myanmar, sun shiga halin rana zafi, inuwa kuna, a matsyinsu na ’yan gudun hijira a Bangladesh.

Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa irin tsanar da ake nuna musu a kauyukan da suke gudun hijira ta sa sun fara tunanin komawa gida, duk da cewa a can suna fusknatar barazanar kisan kiyashi daga sojoji.

Noor Kamal na daga cikin dubban Musulmin Rohingya da suka yi  gudun hijira daga Myanmar zuwa Bangladesh, bayan sojojin Myanmar sun rika bin kauyukansu suna karkashe su — matakin da Majalisar Dinkin Duniya ke bincike a kansa a matsayin kisan kare dangi.

Kamal Noor ya ce, “Ana yawan nuna mana tsana a kafofin yada labarai da kuma ’yan yankunan da muke zama, wanda ya sa nake fargabar nan gaba abin zai iya kaiwa ga tashin hankali.”

Gara mun koma gida —’Yan Rohingya

Ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a sansanin da suke gudun hijira a kan iyakar Bangladesh, cewa sun fara tunanin komawa Myanmar.

“Gara kawai mu koma gida, ko da ruwan harsasai za a yi mana; akalla idan an kashe mu, za a binne mu kasar ta iyaye da kakanni,” in ji shi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da Musulmin Rohingya 750,000 ne suka tsere zuwa kasar Bangladesh sakamakon kisan kiyashin da sojojin Myanmar ke musu a kauyukansu.

A baya, dubban Musulman Bangladesh da kisan gillar da ake wa Musulmin Rohingya a Myanmar, yake ba su takaici kan yi tafiya mai tsawo a fadin kasarsu domin rarraba wa ’yan gudun hijirar kayan tallafi, abinci da magunguna.

Sauyin fuska

Sai dai a baya-bayan nan, halayyar ’yan Bangladesh ta sauya a gare su, bayan an shafe shekaru ba tare da cim-ma nasara a kokarin mayar da su kasar Myanmar ba.

Lamarin ta kai ga kafofin yada labarai da ’yan siyasar Bangladesh sun kafa musu kahon zuwa tare da zargin su da zama barazanar tsaro da kuma dillancin miyagun kwayoyi.

Gwamnatin Bangladesh ta yi gagarumin kokari wajen tallafa wa masu gudun hijirar, gami da tallafin kudade daga Majalisar Dinkin Duniya domin kula da su.

Sai dai kuma ta ce, duk da tallafin da na wasu hukumomin jinkai na kasa da kasa, tana fama da matsalolin gudanarwa da na tsugunar da ’yan gudun hijirar.

Abin ya gagae mu —Sheikh Hasina

A watan Satumba, Fira Ministan Bangladesh, Sheikh Hasina, ta ce dawainiyar kula da sansanin ’yan Rohingya ta zama wata babbar kalubale ga aljihun gwamnatin saboda makuden kudaden ta take kashewa.

Ta ci gaba da cewa hakan kuma barazana ce ga samun daidaito ta fuskar siyasara kasar.

“Idan matsalar ta ci gaba… za ta iya shafar bangaren tsaro da zaman lafiya a daukacin yankin,” kamar yadda ta shaida wa Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York na kasar Amurka.

Bugu da kari, yujin mulkin da sojoji suka yi a Myanmar ya kara kawo babban tasgaro ga yiwuwar ci gaba da maganar mayar da su kasar a nan kusa.

Sun kwace mana ayyuka —’Yan Bangladesh

Da alama dai zaman ’yan Rohingya ya gunduri mazauna yankunan da ke makwabtaka da sansanonin da aka tsugunar da su.

’Yan kasar na ganin bakin sun zauna fiye da kima kuma sun gaji da su.

“Suna janyo wa Bangladesh abin kunya, ya kamata a tisa keyarsu zuwa Myanmar ba tare da bata lokaci ba,” a cewar kakakin wata kungiyar fararen hula ta kasar, Ayasur Rahman.

Ya shaida wa AFP cewa, suna zargin ’yan gudan hijiar, “Sun kwace mana ayyuka sannan suna amfani da takardun fasfo din kasarmu.”

Barazanar tsaro

A hannu guda, kafofin yada labaran kasar na yawan yin sharhi a kan abin da suke kira barazanar tsaro a sansanoni ’yan gudun hijirar da kuma hadarinta ga kasar.

A watan Agusta, a lokacin zagayowar cika shekara biyar da kisan kiyashin da sojojin Myanmar suka yi, wanda ya tilasta wa ’yan Rohingya tserewa zuwa Bangladesh, wata fitacciyar kafar yada labaran intanet a Bangladesh ta yi wani sharhi mai taken, ‘Sai yaushe za a bar azabar da Banladesh saboda karamcinta?’

Wata kafar yada labarai kuma ta yi wani labari da takensa ya siffanta zaman Rohingya a Bangladesh da ‘mugunyar cutar kansa’.

Karuwar yadda kafafen yada labaran kasar ke aibata bakin ya kai matakin  suka ja hankalin Shugabar Hukumar Kare Hakki ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet, a ziyarar da ta kai Bangladesh a watan August, gabanin barin ta ofis.

Ta ce, “Yawan labaran kin jinin Rohingya Bangladesh da na gani sun ya dame ni sosai.

“Bugu da kari ana musu kudin goro wajen suka da muzantawa tare da daukar mataki a kansu bisa zargin su da zama silar manyan lafiuka a kasar,” in ji ta a lokacin.

Akwai ban takaici

Wasu daga cikin ’yan gudun hijirar sun bayyana cewa ana samun tashin hankali da ayyukan laifi a sansanin Kutupalong — duk da cewa abin yana karewa ne a kan ’yan Rohingya.

Kungiyar sojojin sa-kai ta Arakan ta ’yan Rohingya (ARSA), wadda a baya ta gwabza fada da sojojin Myanmar tana kokarin kwace ikon gudanar da sansanonin gudun hijirar.

Sa-in-sa tsakaninsu da jami’an kungiyoyin fararen hula da ke jayayya da su kan sa su hallaka jami’an.

Kudancin Bangladesh kuma yanki ne da ya yi kaurin suna wajen safarar kwayar methamphetamine daga Myanmar, kuma Rohingya akan yi amfani da ’yan Rohingya a masayin ’yan aike domin isar da kwayar ga manyan dilolinta a Bangladesh.

Duk da cewa harka ta safarar kwaya an faro ta ne tun kafin 2017 da Rohingya suka tsere zuwa kasar ba, amma sun ce ana yawan zargin su tare da yi musu a fadin Bangladesh.

“A cikin mutum miliyan daya, ba za a rasa tsirarun bata-gari ba, amma ba adalci ba ne saboda haka a yi daukacin ’yan gudun hijira kudin goro a matsayin masu aikata laifi.” Rohingya refugee Abdul Mannan told AFP.

“Abin bakin ciki ne matuka yadda ake kallon miyagun iri,” in ji wani dan gudun hijira, Abdul Mannan, a zantawarsa da AFP.

Tsadar rayuwa

A bana, matsin tattalin arziki da ya haifar da tashin gwauron kayan masarufi da daukewar wutar lantarki a Bangladesh sun haifar da zanga-zanga.

Kasar ta kuma fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni da ta mamaye gidaje tare da yanke wasu kauyuka daga sassan kasar.

Hakan ya kawo koma baya ga karamci da irin tallafin da jama’ar kasar ke kaiwa sansanonin gudun hijira.

Wani Farfesa a Fannin Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar Illinoi ta kasar Amurka, Ali Riaz, ya ce, “Tausayawar da ake nuna wa bakin a 2017 da shekarun da suka biyo baya ta ragu.

“Yanzu batun kin jinin baki ya maye gurbinta,” in ji masanin, wanda ya yi rubuce-rubuce da dama kan matsalar Rohingya.

Ya shaida wa AFP cewa, yanzu, “Tsana da zullumi su ake nunawa, abin takaicin kuma ba kadan ake yi wadannan abubuwa ba.