A kwanakin baya ne kungiyar Manchester United ta raba gari da kocinta, Ole Gunnar Solskjaer, bayan Watford ta lallasa kungiyar da ci hudu da daya bayan ya yi shekara uku yana da horar da ’yan wasan kungiyar.
A jawabinsa na ban kwana, tsohon dan wasan na Man United ya ce, “Ina alfahari da damar da na samu ta horar da wannan kungiya mai tarihi. Ta kofar gaba zan fita domin ina da yakini magoya bayan kungiyar sun san na yi iya kokarina.”
- Gwamnatin Tarayya za ta raba wa mata rishon girki
- Kidayar ’yan Najeriya za ta lakume N190bn a badi — Majalisa
Solksjaer ne koci na hudu da ya horar da ’yan wasan kungiyar bayan tafiyar Sir Alex Ferguson a karshen kakar 2012-2013.
Tun bayan tafiyarsa ake ta canja koci-koci, amma har yanzu ba a samu nasarorin da ake bukata ba.
Wannan ya sa Aminiya ta yi tariyar zamanin kowane koci da yadda ta kaya a lokacinsa.
A Nuwamban shekarar 1986 ne Sir Alex ya karbi ragamar horar da Manchester United, sannan ya yi ritaya a shekarar 2013.
A zamaninsa, ya jagoranci kungiyar a wasanni guda 1,301, inda ya yi nasara a wasanni 798, ya yi kunnen doki a wasanni 274, sannan aka doke shi a wasanni 229.
Sannan ya lashe Gasar Firimiyar Ingila 13 da Gasar Cin Kofin FA 5, Community Shield 10 da Zakarun Turai biyu da European Cup daya da European Super Cup daya da FIFA Club World Cup da Intercontinental Cup 1.
David Moyes (Yuli 2013 zuwa Afrilu 2014)
Sir Alex Ferguson ne ya bayar da shawarar a dauko David Moyes a matsayin wanda zai maye gurbinsa bayan ya yi ritaya a lokacin yana da horar da kungiyar Everton.
A zamaninsa ya jagoranci kungiyar ta buga wasa 51, inda ya lashe wasa 26, ya yi kunnen doki 10 sannan aka doke shi a wasa 15.
Moyes ya lashe kofin FA guda daya a zamaninsa.
Daga cikin ’yan wasan da ya sayo akwai Juan Mata da Fellaini da sauransu.
Louis van Gaal (Yuli 2014 zuwa Mayu 2016)
Bayan an sallami Moyes, sai kungiyar ta dauko Van Gaal wanda fitaccen koci ne a duniyar tamaula.
Ya jagoranci kungiyar a wasanni 103, ya samu nasara a wasanni 54, ya yi kunnen doki a wasanni 24 sannan ya yi rashin nasara a wasanni 25.
Shi ma a zamaninsa ya lashe kofin FA.
Daga cikin ’yan wasan da ya saya akwai Anthony Martial da Luke Shawa da Angel Di Maria da sauransu.
Jose Mourinho (Mayu 2016 zuwa Disamba 2018)
Bayan Van Gaal, sai Mourinho ya karbi ragamar kungiyar bayan ya raba gari da Real Madrid.
A zamaninsa ya buga wasanni 144, ya lashe wasanni 84, ya yi kunnen doki 31 sannan aka doke shi a wasa 29.
Ya samu nasarar lashe kofuna 3: Euopa 1 da League Cup da FA Community Shield.
Daga cikin ’yan wasan da ya kawo akwai Zlatan Ibrahimovic da Alexis Sanches da sauransu.
Za a yi cewa Mourinho ne ya dan tabuka, inda akalla ya lashe kofuna uku.
Ole Gunnar Solskjaer (Daga Dasumbar 2018 zuwa Nuwambar 2021)
Solskjaer ne ya maye gurbin Mourinho, inda magoya bayan kungiyar suka fara sa tsammani ganin ya fara da kafar da dama.
Sai dai jim kadan sai abubuwa suka fara lalacewa.
A zamaninsa ya buga wasa 168, inda ya samu nasara a wasa 92, ya yi kunnen doki 35, sannan aka doke shi a wasa 41.
Sannan kuma bai lashe kofi ko daya ba.
Daga cikin ’yan wasan da ya sayo akwai Bruno Fernandes da Donny van der Beek da Cristiano Ronaldo da sauransu.
Ina aka dosa?
Michael Carrisk wanda tsohon kyaftin din kungiyar ne, kuma tsohon Mataimakin Koci a zamanin Jose Mourinho da Solskjaer ne ke rikon kwaryar kungiyar.
Za a iya cewa ya fara da kafar dama, domin a wasansa na farko, kungiyar ta doke Villareal da ci biyu da nema a wasan Zakarun Turai.
Daga cikin wadanda ake tunanin za su iya maye gurbin Solskjaer akwai Carrick din, da Pocchetino na PSG da Bregdan Rodgers na Leicester City da sauransu.
Sai dai kasancewar da wahala a samu koci na dindindin a tsakiyar kakar wasanni, kungiyar na neman koci ne wanda zai yi riko zuwa karshen kakar bana.
A ranar Asabar mai zuwa Carrick zai jagoranci kungiyar a wasansa na biyu, inda kungiyar za ta fafata da Chelsea a wasan gasar Firimiyar Ingila.