Iyayen ’yan matan Makarantar Chibok sun koka game da abin da suka kira karairayin da gwamnati take ta sharara musu a tsawon shakera takwas da aka sace ’ya’yan nasu.
Akalla mutum 24 daga cikin iyayen daliban ne aka tabbatar sun rasu sakamakon cutar hawan jini ko bugun zuciya, tun bayan da aka sace daliban su 276 a makarantar kwanan da ke Kudancin Jihar Borno a shekarar 2014.
- Matashiyar da ta yi karyar garkuwa da yi mata fyade ta shiga hannu
- Manyan masu fada a ji a Zamfara na taimaka wa ’yan bindiga —Matawalle
A yayin da ake bikin cika shekara takwas da sace daliban a ranar Alhamis, kungiyar kare hakki ta Amnestyi Interantional ta ce daga lokacin da kungiyar Boko Haram ta sace ’Yan Matan Chibok zuwa yanzu, daliban da aka aka yi garkuwa da su a yankin Arewacin Najeriya sun haura 1,500, yawancinsu ’yan mata.
“Daga cikin ’yan makaranta 1,500 da aka sace a Arewacin Najeriya bayan harin Makarantar Chibok, har yanzu akwai akalla dalibai 120 da ba a sako ba, ba a san makomarsu ba, yawancinsu kuma ’yan mata ne,” inji Sanarwar da Daraktan Amnesty International a Najeriya, Osai Ojigho.”
Da take bayani kan mawucin halin da suka shekara takwas a ciki bayan sace daliban, daya daga cikin iyayen ’yan matan, Rachael Daniel, ta bayyana cewa “Bayan ’ya’yanmu ba ke hannunsu, akwai ’Yan Matan Dapchi da kuma wadanda aka sace a jihohin Zamfara, Kastina da Kaduna.”
Misis Rachael wadda ta yi bayani a yayin da aka cika shekara takwas cur da sace daliban a ranar Alhamis, ta ce ta ce tuni suka debe tsammani daga Gwamnatin Tarayya, sun zura wa sarautar Allah ido.
Garkuwa da dalibai a Najeriya
A ranar 14 ga watan Maris, 2014 ta yi awon gaba da daliban da suke shirin rubuta jarabawar kammala sakandare Makaranta ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Jihar Borno.
Daga cikin daliban an yi sa’a mutum 164 sun tsere ko an kubutar da su ko an gano su a wasu wurare, wasu 16 kuma sun riga mu gidan gaskiya.
Aminiya ta gano a halin da ake ciki, shekara takwas bayan faruwar lamarin, har yanzu akwai sauran dalibai 109 da ke gannun kungiyar ta Boko Haram.
Tun bayan harin Makarantar Chibok, kungiyar Boko Haram ta dauki salon yin garkuwa da mutane masu yawa, musamman dalibai, inda daga baya ta sace wasu dalibai kimanin 1oo makarantar sakandaren ’yan mata da ke Dapchi a Jihar Yobe.
Daga baya an yi nasarar ceto ’Yan Matan Dapchi, in banda guda daya, Leah Sharibu, bayan tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar.
A shekarun baya-bayan nan kuma ’yan bindiga da suka addabi yankin Arewa maso Yammaci da Arewa ta Tsakiya sun dauki salon sace dalibai domin karbar kudin fansa.
Na karshe-karshen nan shi ne wanda a Jihar Zamfara ’yan bindiga suka sace dalibai mata na Kwalejin Kimiyyar Lafiya da ke Karamar Hukumar Tsafe a jihar.
An rufe makarantu 11,536
Amnesty International ta ce, “Daga watan Disamban, 2020 zuwa Oktoba 2021 kadai an yi garkuwa da dalaibai 1,436 da malamai 17 a makarantunsu a Najeriya.
Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ya ce matsalar tsaro da hare-haren ’yan ta’adda sun yi sanadiyyar rufe makarantu akalla 11,536 daga shekarar 2020 a Arewacin Najeriya.
UNICEF ta kara da cewa hakan ya haifar da matsala ga ilimin yara akalla miliyan 1.3 a yanin Arewancin kasar.
Misis Rachael Daniel ta ce, “Muna rokon su, don Allah su yi duk abin da za a yi ’ya’yanmu su dawo; sai kuma idan laifi ne mu tura ’ya’yanmu makaranta? Muna son a dawo mana da ’ya’yanmu a raye kuma cikin koshin lafiya.
“Allah muke jira Ya kawo mana dauki, shekara takwas ke nan da sace ’yata Rose, shekara takwas ina cikin damu, babu ranar da za ta zo ta wuce a tsaron lokacin nan ba tare da na yi tunaninta ba.
“Yanzu Allah kawai muka mika wa al’amarin, amma duk wasu alkawura da aka yi mana sun zama kamar an shuka dusa.”
Gwamnati ta gaza
Kakakin Kungiyar Iyayen ’Yan Matan Chibok, Mista Alanson Ayuba, ya zargi Gwamantin Tarayya da yi musu alkawarin karya game dawowar daliban.
Ya kuma soki gwamnatin kan yadda mayakan Bokon Haram da suka sace ’yan matan ko suka aurar da su suke mika wuya amma ba tare da ’yan matan ba.
“Muna so Gwamnatin Buhari ta gaya mana, ina ’ya’yanmu suke? Dubban wadanda suka yi wannan zamamin aiki na ta mika wuya amma ba tare da an ga ’ya’yanmu ba, to ina ’ya’yan namu suke, ina aka kai su? Ina Leah Sharibu? Muna neman amsar wadannan tambayoyi.
“Kowannensu ya tuna cewa zai yi bayani a gaban Allah; har yanzu akwai sauran ’Yan Matan Chibok 110 da ba san inda suke ba, mun gaji da wadannan alkawuransu da karairayi da farfaganda.
“Abin da muke so kawai shi ne a gaggauta sako mana ’ya’ya, wasunmu sun rasu saboda sace ’ya’yansu, wasu kuma sun kamu da rashin lafiya saboda rashin sanin inda yaran suke.
“Gwamnati ta fito kawai ta yi abin da ya dace wajen ganin an sako ragowar ’Yan Matan Chibok 110 da kuma Leah Shaibu,” inji Mista Ayuba.