Sarki na jin haka, bai yi wata-wata ba ya aika aka kira masa tsoho. Tsohon ya bukaci zai tafi da yaron yawon neman ilimi don ya koya masa wasu darussa. Nan take Sarki ya amince.
Tsoho da dan sarki suka kama hanya zuwa cikin wani daji. Sai tsohon ya ga wata shuka sai ya ce yaron ya cire ta, nan take dan sarki ya tuge shukar ba tare da wata matsala ba.
Sun matsa gaba kadan sai suka hangi wata bishiya, nan take tsoho ya umarci yaron ya tuge karamar bishiyar. Sai da yaron ya dauki lokaci kankane kafin ya tuge bishiyar. Daga nan suka ci gaba da tafiya, sai suka hangi wata katuwar bishiya. Nan take tsoho ya kalli yaron ya umarci ta je ya tuge bishiyar da hannunsa ba tare da amfani da gatari ko magirbi ba.
Dan Sarki ya yi iyakar iyawarsa don ya tuge bishiyar amma hakan ya gagara. Nan take ya shaida wa tsoho cewa ba zai i ya tuge wannan katuwar bishiya ba.
Mu kwana nan