Barkamu da warhaka Manyan gobe. Tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari ne a kan “Hali mara kyau”. Labarin ya yi nuni ga yadda aka yi dabara wajen canza halin wani yaro wanda ba shi da kyau.
Akwai wani Sarki a wani kauye wadda yake da da mai hali mara kyau. Kullum sai an kai dan kara wajen Sarkin saboda halaye marasa kyau da yake nunawa. Idan ba a kawo kararsa daga makwabta ba, to za a kawo kararsa daga wata anguwa.
Abin ya addabi Sarkin sai ya shiga neman yadda zai yi ya sanya dan nasa don ya daina aikata wadannan halaye marasa kyau.
Ana cikin hakan sai labari ya isa wajen sarki cewa akwai wani tsoho mai ilimi kuma ana kyautata zaton zai taimakawa dan Sarkin komawa tafarki mai kyau na aikata ayyukan alheri da za a rika yabonsa a maimakon aibanta shi.
Sarki na jin haka, bai bata lokaci ba ya aika aka kira masa tsoho.
Tsoho ya bukaci a ba shi yaron don su shiga duniya neman ilimi. Nan take Sarki ya amince da hakan.
Tsoho da dan sarki suka kama hanya zuwa cikin wani daji. Sai tsoho ya ga wata shuka sai ya umarci yaron da ya cirota, nan yaro ya ciro ba tare da musu ba.
Sun yi gaba kadan sai suka hadu da wata karamar bishiya. Nan ma tsoho ya umarci yaro ya tuge bishiyar/ Yaron ya dan dauki lokaci kafin ya tuge ta.
Da suka matsa gaba, sai suka iske wata katuwar bishiya. Nan tsoho ya umarci yaron da ta tumbuke bishiyar. Yaro ya yi, ya yi, amma ina ya kasa.
Sai tsoho ya ce na ga saboda ka kasa tunbuke wannna bishiya kamar ranka ya baci. To haka halayyar da kake nunawa a kauyenku take batawa mutanenka rai.
Nan take yaro ya gane abin da tsoho ke nufi. Tun daga ranar ya koma nagari inda ya zama yaron kirki kuma kowa yana yabonsa.
Mahaifinsa Sarki ya yi matukar farin ciki da ya ga dansa ya shiryu, ya zama abin koyi a garin.
Da fatan Manyan gobe za su rika zama nagari abin koyi a cikin al’umma