A rayuwarmu ta yau din nan a kasarmu Najeriya, idan akwai abin da ya fi komai karanci shi ne halin kyautata wa juna. A rayuwarmu ta kashin kanmu, babu kyautatawa, haka ma a rayuwarmu ta yau da kullum tsakaninmu da sauran al’umma, wato wajen mu’amala ko aiki ko sana’a, babu kyautatawa. Ba kyautatawa ba kadai, ba mu daraja juna, musamman karami ba ya ganin girman babba, balle ma mu rika kula juna cikin kyautatawa. Irin wannan sai dai a cikin sojoji, nan ma domin ya zama dole, nan ne za ka ga karami yana daraja na gaba.
Wani abin da zai ba ka mamaki kuma ya ba ka takaici, sai ka je asibitocinmu, inda nan ne za ka ga rashin kyautatawa ta karshe. Nan ne za ka malaman jinya ba su nuna kyautatawa, ba su nuna tausayi ga majinyata. Shin haka da ma aka koya masu a lokacin da suke makaranta, yayin da suke nazarta da sanin makamar aiki? A lokacin da mai juna biyu ke cikin madoduwar ciwo da turmutsutsun zafin haihuwa, maimakon ta samu kalamai masu kwantar da hankali daga unguwar zoma a asibiti, sai dai ka ji tana zaginta, tana wulakanta ta. Akwai ma wata unguwoar zomar, wacce kunya ta yi wa karanci, sai ka ji tana cewa: “Lokacin da kika ji dadi da mijinki, ba ki san akwai ranar haihuwa ba?” Don Allah ina ranar wannan abin takaici?
Idan ka bar asibiti, wani wuri kuma da halin kyautatawa ya yi wa karanci, shi ne idan ka je tashar mota. Direbobi da yaran mota, suna yi wa halin da’a karan tsaye. Nan ne za ka ga yadda ake rashin mutunci da isgilanci ga fasinjoji, ba tare da mutunta dan Adam ba. Ko mace ko namiji, yaro ko babba, madamar a tashar mota ne, to idan kana son kanka da arziki, sai ka yi kaffa-kaffa wajen mu’amala da yaran mota, idan ba haka ba kuwa, to tozartawa ba abin komai ba ne a ga yaran mota.
Shin wai mu a Najeriya, me ya same mu ne? Ta yaya za a ce hatta bangaren masu mulkinmu da ’yan siyasarmu, nan ma babu kyautatawa? Za ka ga dan siyasa, ba zai tashi kula jama’a ba sai lokacin zabe ya karato. Daga nan kuwa ba ka kara yin arba da shi. Idan ya zo wucewa, motarsa lullube take da bakin gilashi, shi yana ganinku, alhali ku ba ku iya ganinsa. Bai kuma tsaya ba balle ma ku yi musabaha, ku gaya masa matsalolin yankinku.
Kyautatawa kuwa halayya ce mai kyau, halayya ce da ke yaukaka zumunci da tabbatar da dadin zamantakewa da juna. A yayin mu’amala da mutane, yana da kyau mu rika sanya hikima da da’a da kyautatawa. Halayya ce marar kyau a ce mutum zai yi mu’amala da mutane alhali yana nuna kyama da rashin ladabi ga na gaba ko kuma mutum ya ce zai rika rainawa da wulakanta jama’a.
A rayuwa, babu abin da zai karfafa mana zaman lafiya da kwanciyar hankali kamar kyautata wa juna. Wannan kuwa ya hada da yada gaisuwa tsakanin juna. Duk inda ka gamu da mutum, ta wajen aiki ne, a kasuwa ko kuma a makaranta ko kuwa ma a gida, gaisuwa ce za ta karfafa zaman lafiya da kyautata zama tsakanin al’umma. Yaro ya gaishe da babba, na tsaye ya gaishe da na zaune, mai tafiya ya gaishe da na tsaye. Wannan shi ne tsari mai kyau kuma mai karfafa da kyautata mu’amala tsakanin al’umma. A lokacin da mutum ya gaishe ka da wasu kalmomi masu kyau da dadi, hakki ne a kanka kai ma ka gaishe shi da gwargwadon kalmomin ko kuma ma ka kara da wasu masu dadi a sama. Wannan shi ne kyautatawa.
Hatta sunnar Manzon Allah (SAW), ta karfafa mana cewa mu lizimci kyautatawa tsakanin juna, domin mu ji dadin zama da juna. Mu kyautata wa makwabta da bakinmu da suka ziyarce mu. Kyautatawa ce ga bako, idan ya ziyarce ka, ka yi masa rakiya har zuwa bakin kofar gidanka.
Kyautatawa ce ga mutum, ida ya yi maka kyauta ka gode kuma ka bayar da tukwici. Idan ma kana da hali, wanda ya yi maka kyauta, kai ma ka yi masa kyauta da abin da ya fi nasa kima. Wannan ne zai kara dinke al’umma, ya samar da ingantaccen zaman lafiya tsakanin juna, domin kuwa soyayya za ta wanzu tsakanin masu kyautata wa juna. Haka kuma, tausayi da jinkan juna za su wanzu ga al’ummar da ke kyautatawa tsakaninsu.
Aiki ne mai kyau kuma kyautatawa ce ga mutum ya kyautata wa wanda ya munana masa. Idan ka ziyarci wani mutum, amma bai amshe ka da karimci ba, bai ba ka wani abu na dadada rai ba, to kai idan hali ya yi, ya kawo maka ziyara, ka kyautata masa, ka yi masa karimci. Domin ba abu ne mai kyau ba ka ce za ka mayar da mugunta da wata mugunta. Abin da ake son yi shi ne, ka kyautata wa wanda ya munana maka.
Akwai wani sahabi da ya tambayi Manzon Allah (SAW) cewa: “Ya Manzon Allah, idan na kai wa wani ziyara amma bai kyautata mani ba, to ni ya kamata in kyautata masa, ko kuwa in rama abin da ya yi mani?” Manzon Allah (SAW) ya ce masa: “Ka kyautata masa.”
A rayuwarmu, lallai ya dace mu sake nazari, mu dauki halin kyautata wa juna, musamman ma tsakanin miji da mata, da da mahaifi, tsakanin malaman makaranta da dalibai, tsakanin shugabanni da mabiya; mu kasance masu kyautata wa juna. Ta haka ne rayuwa za ta yi dadi, a samu wanzuwar da’a da soyayyar juna; wanda haka zai wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu.
Halayyar kyautatawa ta yi karanci a cikin al’umma
A rayuwarmu ta yau din nan a kasarmu Najeriya, idan akwai abin da ya fi komai karanci shi ne halin kyautata wa juna. A rayuwarmu…