Jami’an tsaro a jihar Zamfara sun kama tare da killace mutum 251 da ake zargi da hakar zinare ba bisa ka’ida ba.
Rundunar hadin gwiwar ‘yan sanda sun gabatar da wadanda aka kama din domin kammala bincike.
Da yake yi wa manema labarai bayani a yau Jumu’a, Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Usman Nagogo ya ce masu hakar zinaren ba bisa ka’ida ba sun kunshi ‘yan kasar China da ‘yan Najeriya.
Usman Nagoggo ya ce shi da kansa ya jogaranci zuwa wurin hakar zinaren da aka kama mutanen a Kwalli, karamar hukumar Bukuyum.
- PDP ta yabi yadda Buhari ya tunkari ‘yan bindiga a Zamfara
- An sake kama ‘yan China masu hakar ma’adanai a Najeriya
A cewarsa mutanen na yin hadin gwiwa ne wurin hakar zinaren ta haramtacciyar hanya a jihar.
Ya ce tuni aka mika mutanen zuwa hedikwatar ‘yan sandan ta kasa da ke Abuja domin cigaba da bincike.
Kwamishinan ya kara da cewa Babban Kwamandan Birget na 1 da jihar, O.M. Bello ya jagoranci wani samamen hadin gwiwa da jami’an ‘yan sandan ciki zuwa wasu mahakan zinare a kananan hukumomin Anka da Gummi da kuma Bukuyyum a inda suka cafke mutum 251.
Abubuwan da aka kwace daga hannun mutanen sun hada da injinan samar da ruwa, babura, da sunadaren wanke zinare.
“Ina gargadi mutane cewa an haramta hakar ma’adanai a jihar har sai lokacin da gwamnati ta dage dokar.
“Duk wanda aka kama za’a hukunta shi,” inji shi.
Idan dai za a iya tunawa ko a ‘yan makonnin da suka gabata rahotanni sun nuna yadda aka kama wasu ‘yan Chinan bisa zargin hakar ma’adinai a jihar Osun ba bisa ka’ida ba.